Ahmad Lawan Ya Caccaki Masu Sukar Majalisa, Ya Nemi Yan Najeriya Su Musu Adalci
- Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ke sukar majalisa babtare da sanin ayyukanta ba
- Sanatan yace kamata yayi masu sukar majalisar dokoki su duba ayyukan da sukayi su soke su akansu ba wai da ra'ayi ba kawai
- Yace da yawan waɗanda ke sukar yan majalisu ba su san ainihin aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora wa yan majalisun ba
Shugaban Sanatoci, sanata Ahmad Lawan, a ranar Laraba ya roƙi waɗanda ke sukar majalisa da cewa basa iya komai sai yadda aka juya su, su musu adalci, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba
Sanatan yace idan za'a musu hukunci to a duba ɗumbin ayyukan alherin da suka yi ba wai da ra'ayi ba.
Lawan ya bayyana hakane yayin da ya karɓi baƙuncin wakilan ƙungiyar masu shirya wasan kwaiwayo na arewa, waɗanda suka kai masa ziyara a lzauren majalisa, Abuja.
Yace majalisa ta tara zata cigaba da aiki kafaɗa-da-kafaɗa da majalisar zartarwa domin tabbatar da an yiwa yan Najeriya aiki nagari.
Yace: "Idan wani yana tunanin cewa, sai an samu rashin jituwa tsakanin majalisar dokoki da majalisar zartarwa sannan zai yarda muna aiki, to wannan mutumin bai san abinda yake yi ba."
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu
"Aikin mu shine mu bibiyi ayyukan majalisar zartarwa domin tabbatar da cewa mutane, yan ƙasa sun samu abinda yakamata su samu daga gwamnatin da suka zaɓa da hannunsu. An zaɓe mu ne saboda mu kula da ayyukan da ake zartarwa."
"Idan munga abinda ba dai-dai ba, mu ce nan fa ba haka yake ba, amma gwamnati na yin abinda ya kamata shiyasa a koda yaushe muke goyon bayanta.
"Ina roƙon waɗanda ke sukar mu, su duba ɗumbin ayyukan da mukayi, su daina sukar mu da ra'ayinsu kawai." a cewarsa.
Sanatan ya ƙara da cewa wasu yan Najeriyan ba su fahimci miye ainihin aikin yan majalisar tarayya ba, kawai buƙatar su suga ba'a jituwa tsakaninsu da ɓangaren zartarwa.
Lawan yace majalisa zata cigaba da aiki da yan Najeriya, zata daina kula duk wata suka da ake mata domin ta maida hankali wajen sauke nauyin da aka ɗora mata.
"Hakan ba zai hana a ƙalubalance mu ba, idan kana ganin munyi ba dai-dai ba, kofar mu a buɗe take kazo ka faɗa mana inda nuka yi kuskure tare da dalilanka, sannan ka bamu shawarar yadda zamu gyara." inji Lawan
A wani labarin kuma Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja
Ana cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar a ƙauyen Paiko biyo bayan tsintar gawarwakin wasu fulani makiyaya a dajin dake yankin.
Wani mazaunin garin mai suna Musa, yace an gano makiyayan da raunukan harbin bindiga a jikinsu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng