El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba

El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba

- Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ya kamata Najeriya ta daina dogara da albarkatun man fetur

- Gwamnan yace akwai hanyoyi da dama da za'a iya bi domin tattara bayanan kowane ɗan Najeriya sannan a sanya mishi haraji

- A cewarsa a halin yanzu hukumar tara kuɗin haraji ta ƙasa da kwastam sune kaɗai ke ceto Najeriya wajen tara mata kuɗin shiga

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yace karɓar haraji, ba kuɗin man fetur ba, zai iya ceto tattalin arziƙin ƙasa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

Yayin da yake jawabi a wajen taron haraji na shekara-shekara karo na 23 a Kaduna, gwamnan yace kasar data dogara da haraji tafi yin aiki yadda ya kamata.

Yace ya kamata Najeriya ta fara shirye-shiryen dena dogara da albarkatun man fetur domin ba itace hanyar da zata warware matsalolin kasar ba.

El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba
El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Malam Nasiru yace:

"Hanyar warware matsalar kuɗaɗen shiga da ƙasar nan ke fama da ita itace sanya haraji kan kowanne kayayyaki domin farfaɗo da tattalin arziƙi."

Gwamnan yace a halin yanzu ana ƙarɓar haraji ne daga hannun mutane ƙalilan a Najeriya, amma akwai hanyoyin da ya kamata abi domin samun bayanan dukkan yan Najeriya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Zan Hukunta Ku Yadda Ba Zaku Sake Sha’awar Dawowa Kaduna Ba, El-Rufai Ga Shugabannin NLC

Yace: "Za'a iya samun bayanan yan Najeriya domin ƙarɓar haraji daga hannunsu ta hanyoyi kamar lasisi tuƙi na ƙasa, lambar sirri ta banki (BVN), da kuma hukumar samar da katin zama ɗan ƙasa (NIMC)."

"Kwamishinan kuɗi ya sanar dani cewa a taron majalisar rarraba kuɗaɗen shiga (FAAC) na watan da ya gabata, hukumar tara kuɗin haraji ta ƙasa da kwastam sune suka ceci Najeriya."

"Hakanan an sanar dani cewa taron FAAC na wannan satin da muke ciki, ana tsammanin NNPC ba zata kawo komai ba. Sabida haka ko muna so ko bama so dole mu daina dogara da albarkatun man fetur."

Gwamnan yace saboda wannan tallafin man fetur ɗin da gwamnatin Najeriya ke biya yasa NNPC bata iya tara komai a ɓangaren kuɗaɗen shiga.

Ya kuma bada shawarar cewa sanya haraji ga kowanne ɗan Najeriya itace hanya mafi sauƙi wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.

A wani labarin kuma Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja

Ana cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar a ƙauyen Paiko biyo bayan tsintar gawarwakin wasu fulani makiyaya a dajin dake yankin

Wani mazaunin garin mai suna Musa, yace an gano makiyayan da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel