Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Halaka Direba Sannan Suka Sace Fasinjoji 13 a Nasarawa
- Wasu yan bindiga sun tare motocci a Nasarawa inda suka kashe direba suka sace fasinjoji 13
- Wani direba da motarsa ke bayan wadanda abin ya ritsa da su ya ce karar bindiga da ya ji yasa ya juya motarsa ya gudu
- Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel ya ce ba a tuntube shi an sanar da shi game da lamarin ba
Yan bindiga sun kashe wani direba mai suna Adamu Usman sun kuma sace fasinjoji 13 a kan hanyar Shafa-Abakpa-Umaisha a karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa, Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa an harbi marigayin sau uku ne a cikinsa kuma ya rasu ne a lokacin da ake masa magani a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Abuja a daren ranar Talata.
DUBA WANNAN: Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari
Ibrahim Saidu, wani direba da ya tsallake rijiya da baya a harin ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 5 na yamma.
Ya ce masu garkuwar sun fito daga daji ne suka tare motocci hudu da ke zuwa daga kauyen Ugya.
Ya ce motoccin sun dako fasinjoji ne za su kai su Abaji da Toto a lokacin da harin ya faru.
Saidu ya ce masu garkuwar sun zagaye motoccin ne bayan motar ta kwace wa direban sannan suka yi awon gaba da fasinjoji 13 ciki har mace mai matsakaicin shekaru suka shiga daji.
"Ni ke biye da motoccin hudu amma Allah ya kiyaye ni lokacin da na tsaya a wani kauye domin daukar fasinja. Da nake tahowa sai naji karar bindiga hakan yasa na juya nan take," in ji shi.
KU KARANTA: Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel ya ce ba a tuntube shi an sanar da shi game da sace fasinjojin ba.
Ya ce zai tuntubi DPO na karamar hukumar Toto ya nemi karin bayani kafin ya yi magana game da lamarin.
A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.
Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.
Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.
Asali: Legit.ng