Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna

Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna

- Kamfanin rarrabe wutar lantarki na kasa ya sanar da dawowa jihar Kaduna ta wuta

- Kamar yadda mai magana da yawun kamfanin ya fitar, yace sun yi hakan ne bayan NLC ta janye yajin aiki

- Takardar ya kara da tabbatar da cewa kamfanin zai cigaba da sakin wuta a hanyoyin samuwarta ta karkashi KAEDCO

Kamfanin rarrabe wutar lantarki ta Najeriya (TCN) ta dawo da wutar lantarkin jihar Kaduna, sa'o'i kadan bayan kungiyar kwadago ta kasa ta janye yajin aikin jan kunne da ta shiga a jihar.

TCN ta sanar da dawo da wutar lantarkin a wata takardar da mai magana da yawunta, Ndidi Mbah ya fitar a shafin kamfanin na Twitter.

"TCN ta dawo da samar da wutar lantarki ta hanyoyin samar da wutanta a jihar Kaduna. Hanyoyin sun hada da: Mogadishu, Abakwa, Sansanin NAF, Unguwan Dosa, Turunku, Arewa, Filin jirgi, Kinkinau, Narayi da sauransu.

KU KARANTA: Tsohon sirikin Shugaba Buhari ya magantu a kan nemansa da ICPC ke yi

Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna
Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kudaden da aka wawure: FG ta samo sama da $700m a cikin shekaru 4, Malami

"Hanyoyin samar da wuta na Jaji da Rigasa na kan hanya yayin da na Olam, PAN da UNTL suke kan hanyar samuwa.

"Hanyoyin wutan gidajen ruwa sun fara tashi amma an datse su saboda matsalar da suka samu ta bangaren KAEDCO.

“TCN za ta cigaba da samar da wutar lantarki ga sauran hanyoyin matukar KAEDCO ta nuna gamsuwarta na samar da wutan," takardar tace.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce wadanda suka katse kasuwanci a jihar da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu.

A cikin kwanakin da suka gabata, mambobin kungiyar kwadago ta kasa da El-Rufai sun yi artabu a kan hukuncin gwamnatin jihar na sallamar sama da ma'aikata 4,000 a jihar.

A sakamakon hakan, kungiyar kwadago karkashin shugabancin Ayuba Wabba ta shiga yaji aikin kwanaki biyar wanda ta fara a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Wannan hukuncin bai yi wa El-Rufai dadi ba wanda ya bayyana cewa yana neman Wabba da sauran 'yan kungiyar kwadagon ruwa jallo a kan abinda ya kwatanta da zagon kasa ga tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel