Zan Hukunta Ku Yadda Ba Zaku Sake Sha’awar Dawowa Kaduna Ba, El-Rufai Ga Shugabannin NLC

Zan Hukunta Ku Yadda Ba Zaku Sake Sha’awar Dawowa Kaduna Ba, El-Rufai Ga Shugabannin NLC

- Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya sake yin kakkausan kashedi ga shugabannin ƙungiyar ƙwadugo NLC

- Gwamnan yace babu wanda aka hana shiga yajin aiki, amma ba zai yuwu dan ka shiga yajin aiki kuma ka hana wasu gudanar da kasuwancin su ba

- Yace gwamnatinsa zata ɗau mataki a kan duk wanda ya karya doka, kuma ba zasu kara sha'awar dawowa jihar ba da zarar an hukunta su

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewa Ayuba Waba da sauran shuwagabannin ƙungiyar ƙwadugo ba zasu sake sha'awar zuwa Kaduna ba bayan ya hukunta su, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja

Yajin aiki da kuma zanga-zangar da ƙungiyar ƙwaɗugon ta shiga ya shiga kwana na uku a yau Laraba.

Gwamna El-Rufa'i ya faɗi haka ne a wajen taron haraji na shekara-shekara karo na 23 a Kaduna ranar Laraba, ya bayyana shugabannin NLC da 'Masu laifi'

Zan Hukunta Ku Yadda Ba Zaku Sake Sha’awar Dawowa Kaduna Ba, El-Rufai Ga Shugabannin NLC
Zan Hukunta Ku Yadda Ba Zaku Sake Sha’awar Dawowa Kaduna Ba, El-Rufai Ga Shugabannin NLC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan yace abubuwan da NLC keyi a jihar na hana buɗe wuraraen kasuwanci kamar bankuna da gidajen man fetur babban laifine kuma karya doka ne.

A jawabinsa, gwamnan yace:

"Ana ƙoƙarin hana buɗe wuraren kasuwanci a jihar mu, ana ƙoƙarin hana bankuna su buɗe, ana ƙoƙarin hana gidajen mai su buɗe, wannan duk ayyukan laifi ne kuma saɓa doka ne kuma zamu ɗauki mataki."

"Gwamnati na ƙoƙarin bada cikakken tsaro ga dukkan masu kasuwancin da suke buƙatar cigaba da buɗe wuraren su."

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Muna Neman Gwamnan Kaduna Ruwa a Jallo, Duk Wanda Ya Kamo Shi Akwai Tukuici, Inji NLC

"Ba wai muna son hana su yancin shiga yajin aiki bane, kuna da damar yin yajin aikin ku, amma kada kuce zaku hana masu son yin aiki gudanar da aikinsu."

Gwamnan ya cigaba da cewa:

"Baku da damar da zaku kulle wa mutane wuraren kasuwancin su, ba zamu amince da haka ba, kuma a shirye muke zamu ɗau mataki akan duk wanda yayi ƙoƙarin yin hakan."

"Matsayar mu a fili take, doka a fili take, zaku iya yajin aikin ku, amma ba zai yuwu ku tsayar da komai ya daina tafiya ba, idan bazaku yi ba wasu zasu yi."

"Ina san in tabbatar muku da cewa zamu yi rugu-rugu da yajin aikin nan, zamu kamo duk wanda ya karya doka mu hukunta shi. Ina tabbatar muku babu wanda zai sha'awar dawowa jihar mu da zarar mun hukunta su."

Shugaban NLC, Ayuba Waba, ya bayyana cewa a shirye yake gwamnatin tazo ta kama shi, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

A wani labarin kuma Zamu Yi Amfani da Dukkan Ƙarfin Mu Wajen Taimaka Wa Najeriya, Shugaban Faransa

Gwamnatin ƙasar Faransa tayi alƙawarin taimakawa Najeriya iya karfinta domin magance matsalar tsaron dake addabar ƙasar.

Shugaba Emmanuel Macron ne ya bayyana haka a wajen taron ƙasashen Africa dake gudana a Faris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel