Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja

Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja

- Ana cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar a ƙauyen Paiko biyo bayan tsintar gawarwakin wasu fulani makiyaya a dajin dake yankin

- Wani mazaunin garin mai suna Musa, yace an gano makiyayan da raunukan harbin bindiga a jikinsu

- Ba'a samu jin ta bakin kakakin hukumar yanda ta birnin tarayya Abuja ba, sabida bata ɗauki waya ba kuma bata maido da amsar saƙonnin da ka tura mata ba

Ana cikin yanayin tashin hankali a Paiko dake yankin Gwagwalada biyo bayan gano gawarwakin wasu yan fulani makiyaya biyu, kamar yadda Daiytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Jami'an Kwastam Sun yi Ram da Ƙwayoyin Turamol Katan 1,387 a Jihar Rivers

Wani mazaunin Paiko, mai suna Musa, yace an gano gawarwakin makiyayan ne da raunin harbin bindiga a wani daji dake kusa da Paiko da yammacin ranar Lahadi.

Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja
Tashin Hankali, An Tsinci Gawarwakin Wasu Yan Fulani Makiyaya Biyu a Ƙauyen Abuja Hoto: theecologist.org
Asali: UGC

Yace waɗanda aka kashe ɗin sun bar gidajen su da nufin tafiya kiwon dabbobi amma sai wasu mutane da ba'a san ko su waye ba suka kai musu hari.

Ya ƙara da cewa mutuwar makiyayan ya jawo zaman ɗar-ɗar tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyukan dake maƙwaftaka da juna.

Rahoto ya bayyana cewa saboda zaman ɗar-ɗar da tsoro kan jita-jitar cewa makiyaya zasu ɗauki fansa, shugaban Paiko, Alhaji Adamu Mustapha, ya kira taron tsaro cikin gaggawa.

Taron ya samu halartar wakilan jami'an tsaro da shuwagabannin gargajiya dake yankin.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Muna Neman Gwamnan Kaduna Ruwa a Jallo, Duk Wanda Ya Kamo Shi Akwai Tukuici, Inji NLC

Yayin da yake jawabi jin kaɗan bayan fitowa daga taron, Alhaji Adamu, yace:

"Ina son in bayyana muku cewa, ko kai waye, ba zamu zuba ido muna kallo a mayar mana da yankin mu ya zama filin yaki, kashe-kashe da hare-haren ɗaukar fansa a tsakanin junan mu ba."

"Muna roƙon jami'an tsaro su yi gaggawar binciko duk wanda keda hannu a kisan waɗannan mutanen kuma su gurfanar dashi domin ya girbi abinda ya shuka."

Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar manoma da makiyaya su yi rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya a tare da juna.

Kakakin hukumar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, bata ɗaga kira ko ta maido da amsar saƙonnin da aka tura mata ba akan lamarin.

A wani labarin kuma Matsalar Tsaro: Zamu Yi Amfani da Dukkan Ƙarfin Mu Wajen Taimaka Wa Najeriya, Shugaban Faransa

Gwamnatin ƙasar Faransa tayi alƙawarin taimakawa Najeriya iya karfinta domin magance matsalar tsaron dake addabar ƙasar.

Shugaba Emmanuel Macron ne ya bayyana haka a wajen taron ƙasashen Africa dake gudana a Faris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel