Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki

Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki

- Wani dan Najeriya ya bar jama'a baki bude bayan wallafa hotunan gidan Obafemi Awolowo dake Ikenne, jihar Ogun

- Hotunan sassan gidan daban-daban da suka hada da wurin tarihi duk mutumin ya wallafa a Facebook

- Daya daga cikin masu tsokacin cewa yayi yana tsammani jihohin kudu maso yamma zasu gyara gidan tare da mayar dashi wurin bude ido

Wani dan Najeriya mai suna Ayo Ojeniyi ya wallafa hotunan gidan marigayi Obafemi Awolowo a shafinsa na Facebook.

Awolowo mutum ne mai kishin kasa kuma shine firemiyan farko na yankin yammacin kasar nan. An haifeshi a ranar 6 ga watan Maris 1909 kuma ya rasu a ranar 9 ga watan Mayun 1987.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta bankado yunkurin sakin bayanan bogi kan lafiyar kwakwalwar Buhari

Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki
Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki. Hoto daga Ajo Ajeniyi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC

Ga hotunan da Ojeniyi ya wallafa tare da tambayar: "Yaushe rabonku da ziyartar gidan Awolowo dake Ikenne?"

A yayin martani, wani mutum mai suna Niyi Karunwi yace ya yi tsammanin dukkan jihohin yankin kudu maso yamma zasu hadu su gyara gidan tare da shi wurin bude ido.

A kalamansa: "Na yi tsammanin jihohin kudu maso yamma zasu karba gidan tare da mayar dashi wurin shakatawa da bude ido."

Wole Uche Adesanmi tsokaci yayi da: "Kai wannan wuri akwai kyau, zai yi dadin kai ziyara."

Mahmud Mohammed Sagir rubutawa yayi: "An godewa Ubangiji da yake haka tsaf."

A wani labari na daban, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a ranar Talata ya sallami kwamishinoni 25, sakataren gwamnatinsa, shugaban ma'aikatan fadarsa, babban mai bashi shawara a harkar siyasa da sauransu.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, Charles Aniagwu, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jihar, ya ce wannan al'amarin an yi shi ne domin baiwa sabbin jini damar taka rawarsu.

Aniagwu ya bayyana wadanda lamarin ya shafa sun hada da kwamishinoni 25, sakataren gwamnatin jihar, Chiedu Ebie, shugaban ma'aikatansa, David Edevbir, babban mai bada shawara kan siyasa, Funkekeme Solomon, tare da wasu masu bada shawara na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel