Jami’an EFCC sun sha da kyar, sun tsere bayan An tare su a cikin Unguwa da tsakar dare
- Matasa sun tare hanya, sun hana jami’an EFCC fita daga wata unguwa a Osun
- Ana zargin ‘Yan damfara ne su ka yi wannan aiki domin su kare takwaransu
- Daga baya matasan sun shirya zanga-zanga a kan samamen da aka kai masu
Wasu da ake zargin cewa masu zamba cikin aminci ne sun tare hanyoyi, domin su nuna rashin jin dadinsu a game da abubuwan dake faruwa a jihar Osun.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wadannan mutanen da ake zargi da laifin damfara sun gudanar da zanga-zangar ta su ne a babban birnin jihar Osun, Osogbo.
Mutanen da aka fi sani da ‘Yan Yahoo-Yahoo’ sun tare titi ne a kan samamen da jami’an hukumar EFCC suka kai masu cikin tsakar dare a cikin makon nan.
KU KARANTA: An yi wa El-Rufai kaca-kaca a kan bada umarnin kama 'Yan NLC
Masu zanga-zangar sun kunna wuta a hanyar shiga yankin Lameco da ke kan titin Osogbo da Ilobu.
Haka zalika masu matasan sun tare da titin Osogbo zuwa Iwo da ke kusa da otel din Rasco. Hakan ya sa dole matafiya su ka saki titin, suka nemi wata hanyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mazaunan unguwannin Omobolanle, da Lameco, da rukunin gidajen Oroki a Osogbo, sun zanta da ‘yan jarida, suka ce sun ji harbe-harben bindiga a cikin dare.
The Nation ta ce jami’an EFCC sun shiga Adetunji Estate and Hallelujah Estate ne da niyyar cafke wasu da ake zargin ‘yan damfara ne, amma dai ba a dace ba.
KU KARANTA: El-Rufai bai da ikon da zai bada umarni a cafke masu zanga-zanga – Falana
Matasan yankin sun fito sun hana jami’an hukumar EFCC tafiya da wasu motoci 20 da suka karbe daga hannun wanda ake zargi da damfarar mutane ta yanar gizo.
A karshe dole jami’an EFCC suka hakura da motocin nan, su ka tsere domin su ceci rayuwarsu.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya bayyana cewa sun samu labarin abin da yake faruwa tun lokacin da ake hayaniya cikin dare.
Kafin nan kun ji cewa tsohon Surukin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana a kan tirka-tirkarsa da Hukumar ICPC mai yaki da barayin gwamnati.
Alhaji Yau Kumo ya ce ICPC ba ta aika masa goron gayyata ba, sai dai ya ji tace ana nemansa ruwa a jallo bisa zargin ya wawuri kudin daga baitul malin gwamnati.
Asali: Legit.ng