Waye kai: Mutanen Twitter sun dura kan Gwamnan Kaduna a kan umarnin kama ‘Yan zanga-zanga

Waye kai: Mutanen Twitter sun dura kan Gwamnan Kaduna a kan umarnin kama ‘Yan zanga-zanga

- Gwamna Nasir El-Rufai ya bada umarnin kama shugaban NLC, Kwamred Ayuba Wabba

- Mutane sunyi wa gwamnan jihar Kaduna raddi a kan wannan magana a shafin Twitter

- Akwai wadanda suke goyon bayan Malam Nasir El-Rufai, suna ganin gyara ne ya kawo

Mutane suna cigaba da tofa albarkacin bakinsu tun da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci ayi ram da shugaban NLC, Kwamred Ayuba Wabba.

Hakan na zuwa ne a sakamakon yajin-aiki da zanga-zangar da ake yi a jihar Kaduna, saboda sallamar tulin ma’aikata da gwamna Nasir El-Rufai ya ke yi.

Legit.ng Hausa da Daily Trust sun dauko martanin mutane a game da matakin da gwamnatin Kaduna ta dauka na yin shelar a damko mata Ayuba Wabba.

KU KARANTA: Lokacin da El-Rufai su ka yi zanga-zanga tare da 'Yan NLC

Aliyu Kwarbai ya ce: “Shin El-Rufai ya yi zanga-zanga tare da NLC lokacin da aka cire tallafin fetur a 2021? Ya yi zanga-zanga da Buhari ya kara kudin mai daga N87 zuwa N165? Meyasa yake kiran NLC munafukai? A kyale su, su yi aikinsu…”

“Gwamnan Kaduna! Jihar da ake shugabanta tamkar kamfani za ta cefanar da mutanenta. Idan aka koma yi wa al’umma kallon hajjar kasuwanci, za a kauda tausayi wanda shi ne ginshikin shugabanci, a shigo da tashin hankali.” A cewar Halal Police.

Jamilu Maiwada ya ce: “Duk wasu alkaluma da za a kawo, duk wasu bayanai da za ayi, muddin ba za ayi maganar yadda mutanen da aka sallama daga aiki za su cigaba da rayuwa ba, duk shirmen banza ne.”

Illa Bappa ya na goyon bayan gwamnan Kaduna, ya rubuta:

KU KARANTA: Yajin-aiki: Zan kori wadanda su ka biyewa NLC - El-Rufai

Waye kai: Mutanen Twitter sun dura kan Gwamnan Kaduna kan kama ‘Yan zanga-zanga
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

“Canjin da muke bukata, wanda muka zabi Buhari ya kawo mana, shi ne abin da Gwamna El-Rufai yake yi a Kaduna, amma kuma mu na kuka. ‘Dan Najeriya ya na son ayi gyara, amma bai son abin da gyara ya kunsa. A dafa yanzu, a ci yanzu kawai!”

Columbos Gideon ya ce a lokacin da El-Rufai su ka yi zanga-zanga a 2012, babu wanda ya cafke shi. Ya ce: "Duk barnar da 'yan bindiga su ka yi, nawa ka sa a cafke?"

Tunde Olaleye ya na ganin giyar mulki ce ta ke daukar gwamna El-Rufai, ya ja-kunnensa: "Ka tuna cewa mulki ba ya daurewa."

"Ka yi amfani da wannan karfin wajen gano Dadiyata da sauran wadanda su ka bace a jihar ka." inji Ameenu Kutama.

Jiya Femi Falana ya bayyana cewa a dokar Najeriya, gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai bai da ikon da zai bada umarni ga 'yan sanda su cafke masu zanga-zanga.

Falana ya ce ‘Yan Sanda suyi watsi da umarnin Gwamnatin Kaduna a kan kama Ayuba Wabba. Lauyan ya ce idan gwamnan ya na da hujja, ya tafi ofishin 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel