Fitaccen Lauya ya fadi dalilai 3 da su ka sa babu yadda Gwamna El-Rufai zai iya da ‘Yan kwadago

Fitaccen Lauya ya fadi dalilai 3 da su ka sa babu yadda Gwamna El-Rufai zai iya da ‘Yan kwadago

- Femi Falana ya soki umarnin da Gwamnan Kaduna ya fito ya bada a jiya

- Lauyan yace doka ba ta ba Nasir El-Rufai damar kama ‘yan kwadago ba

- Mai kare hakkin Bil Adaman yayi kira ga jami’ai suyi watsi da umarnin

Fitacccen lauya mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana, ya soki gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, na bada umarnin a damke shugabannin ‘yan kwadago.

Femi Falana ya ce gwamnan jihar Kaduna bai da hurumin da zai bukaci a cafke Ayuba Wabba da sauran jagororin kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC.

Jaridar Daily Trust ta rahoto gawurtaccen Lauyan ya na sukar umarnin gwamna Nasir El-Rufai.

KU KARANTA: ‘Yan Twitter sun yi wa Jonathan raddi, sun fadi wadanda ya yi wa azaba

“Jawabin da ya fitar abin da dariya ne domin kowa ya san cewa Kwamred Ayuba Wabba da abokan aikinsa suna kan titunan Kaduna, suna jagorantar zanga-zangar lumuna tare da daukacin ma’aikatan jihar tun jiya. Umarnin nan ba zai yi aiki ba saboda:"

“Dokokin kwadago da kundin tsarin mulki sun ba Kwamred Wabba da sauran shugabannin ‘yan kwadago dama kai-tsaye su gudanar da zanga-zangar lumana, a kan kara korar ma’aikata da ake yi daga aiki a gwamnatin jihar Kaduna.” Inji Femi Falana SAN.

“Sashen dokar sauran laifuffuka ba dokar jiha ba ce, ta gwamnatin tarayya ce. Saboda idan gwamna El-Rufai ya na da hujjar Kwamred Wabba da sauran shugabannin ‘yan kwadago sun saba sashen dokar, sai ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda a Kaduna.”

“Gwamnan bai da ikon da zai ayyana wani da ake zargi da laifi a matsayin wanda ake nema a karkashin kowace irin doka.”

KU KARANTA: NUPENG ta shigo, ta fara yi wa Gwamnatin El-Rufai barazana

Fitaccen Lauya ya fadi dalilai 3 da su ka sa babu yadda Gwamna El-Rufai zai yi da ‘Yan kwadago
Femi Falana SAN Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Fitaccen lauyan ya yi kira ga jami’an tsaro su yi watsi da wannan umarni da Gwamnan Kaduna ya bada na cewa ayi da ram da Ayuba Wabba da ragowar takwarorinsa.

Kawo yanzu ‘yan sanda ba su yi magana game da kiran da gwamnatin jihar Kaduna ta yi a jiya ba.

A jiya kun ji cewa Nasir El-Rufai yana cikin wadanda su ka soki kara farashin fetur da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi a 2012, ya ce ya kamata a saida mai a N40.

Idan za a tuna, irinsu Malam Nasir El-Rufai, Dino Melaye, da Femi Fani-Kayode, sun ci karensu babu babbaka a mulkin PDP, sun yi zanga-zanga, ba tare da an yi masu komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel