Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 25, shugaban ma'aikatansa da sakataren gwamnati

Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 25, shugaban ma'aikatansa da sakataren gwamnati

- Gwamnan jihar Delta ya sallami kwamishinoninsa 25, sakataren gwamnatinsa da kuma shugaban ma'aikatan fadarsa

- Kamar yadda tsohon kwamishina yada labarai na jihar ya sanar, yace gwamnan yayi haka ne domin baiwa sabbin jini damar taka rawarsu a mulki

- Sai dai an sallami Bernard Onomovo ne sakamakon kama shi da aka yi da laifin saka wasu sunayen bogi cikin masu karbar albashin gwamnatin jihar

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a ranar Talata ya sallami kwamishinoni 25, sakataren gwamnatinsa, shugaban ma'aikatan fadarsa, babban mai bashi shawara a harkar siyasa da sauransu.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, Charles Aniagwu, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jihar, ya ce wannan al'amarin an yi shi ne domin baiwa sabbin jini damar taka rawarsu.

Aniagwu ya bayyana wadanda lamarin ya shafa sun hada da kwamishinoni 25, sakataren gwamnatin jihar, Chiedu Ebie, shugaban ma'aikatansa, David Edevbir, babban mai bada shawara kan siyasa, Funkekeme Solomon, tare da wasu masu bada shawara na musamman.

KU KARANTA: Daiɗaita NPA kika je yi ba cigaba ya kai ki ba, Hadiza Bala Usman ga Binta Garba

Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 29, shugaban ma'aikatansa da sakataren gwamnati
Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 29, shugaban ma'aikatansa da sakataren gwamnati. Hoto daga @TheCableng
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Gwamna Okowa ya mika godiyarsa ga dukkansu sakamakon rawar da suka taka a gwamnatinsa na tsawon shekaru shida inda yace sun bada gudumawa wurin samar da cigaba a jihar.

Majalisar zartarwar jihar ta amince da sallamar Bernard Onomovo sakamakon kama shi da aka yi da laifin zuba wasu sunayen bogi a cikin wadanda ake biya albashi a jihar.

Aniagwu ya ce Bernard ya kalubalanci hukuncin inda ya nuna cewa bashi da laifi ko kadan.

Ya ce: "'Yan majalisa sun amince da sallamar Bernard Onomovo wanda ke da hannu wurin saka wasu sunaye a cikin masu albashin jihar.

"Kusan shekaru biyu da suka gabata, an bukaci yayi murabus bayan an bincike shi amma sai yayi karar 'yan majalisar zartarwan inda aka sake bincike aka gano ya aikata laifin.

"An sallameshi ne saboda ya bata lokacin 'yan majalisar kuma ya cigaba da karbar albashi har na tsawon shekaru biyu."

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai a ranar Litinin yayi kira ga mazauna jihar da su kare kansu daga miyagun 'yan bindigan dake kutse suna kai masu hari.

Ortom ya sanar da hakan ne yayin martani ga tambayan manema labarai bayan isarsa Makurdi daga jihar Oyo inda ya halarci taron gwamnonin PDP, ya ce akwai bukatar jama'a su mike tsaye domin baiwa gidajensu kariya.

"Na sanar da jama'a da su baiwa kansu kariya. Ba za ku zauna a gidajenku ba kawai wasu su shigo su kashe ku."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: