Da duminsa: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC

Da duminsa: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC

- Gwamna Nasir El-Rufai ya sha alwashin sallamar dukkan ma'aikatan da suka shiga zanga-zangar kungiyar kwadago a jihar

- Gwamnan ya bayyana cewa, yajin aikin ya shafa bankuna da wurare masu zaman kansu wadanda basu da alaka da gwamnati

- Hakan ta sa ya sha alwashin sallamar dukkan ma'aikatan jinya da malaman jami'ar jihar Kaduna da suka fada yajin aikin

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya sha alwashin sallamar dukkan ma'aikatan jinya da malaman jami'a da suka shiga zanga-zangar kungiyar kwadago a jihar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

El-Rufai ya bayyana cewa ana neman shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba da sauran mambobin kungiyar a kan jagorantar ma'aikata da suka yi a gagarumar zanga-zangar da suka yi kan dokokin gwamnan a jihar da basu yi musu ba.

A yayin fitar da takardar da aka saka hannu a ranar Talata, mai magana da yawun gwamnan, Muyiwa Adekeye, yace gwamnan jihar ya ce ba zai lamunci dauke wutar lantarki, kai hari kan kayayyakin gwamnati da gine-ginensu, rufe asibitoci da kuma sallamar marasa lafiya ta karfi da yaji, kutse kan kayayyakin gwamnati da kuma hana walwala da kungiyar kwadagon ke yi ba.

KU KARANTA: Majalisar wakilai za ta halasta noma da safarar wiwi a Najeriya, Kalu

Da duminsa: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC
Da duminsa: El-Rufai ya sha alwashin koran ma'aikatan da suka yi zanga-zanga da NLC. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Daiɗaita NPA kika je yi ba cigaba ya kai ki ba, Hadiza Bala Usman ga Binta Garba

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, mai magana da yawun gwamnan jihar yace gwamnati za ta sallami ma'aikatan jinya da suke a matsayi kasa da 14 da kuma ma'aikatan jami'ar jihar Kaduna da suka shiga yajin aikin.

"Kokarin rufe ta'addancin da ake yi da sunan yajin aiki bai hana mu gane barnar da ake yi ba wanda ya hada da zagon kasa ga ayyuka masu muhimmanci.

"Hakazalika, gwamnatin jihar Kaduna ba za ta cigaba da rufe ido ba tare da kallon irin tirsasawar da ake yi na hana bankuna aiki da sauran wurare masu zaman kansu wadanda ma'aikatan da kwastomominsu basu da wata alaka da gwamnati ba," takardar tace.

A wani labari na daban, fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yace babu dalilin da zai sa ya bar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya shiga gidansa idan da ya biyo tawagar tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.

Idan za mu tuna jami'an jihar Kaduna dake tabbatar da yaki da bara sun shiga makarantar malamin inda suka kwashe almajirai a shekarar da ta gabata, Vanguard ta wallafa.

Sheikh Bauchi ya sanar da hakan ne a gidansa dake Bauchi a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin tsohon sarkin wanda aka nada Khalifan Tijjaniya a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel