Jami'an Kwastam Sun yi Ram da Ƙwayoyin Turamol Katan 1,387 a Jihar Rivers
- Jami'an hukumar kwastam sun samu nasarar cafke kwayoyin turamol katan 1,387 a jihar Rivers
- Kakakin runduna ta biyu dake yankin tashar jirgin ruwa dake Onne a jihar ne ya bayyana haka a Patakwal
- Yace an boye wasu kwayoyin ne a cikin halastattun kaya domin a samu damar shigo dasu cikin Najeriya
Hukumar kwastam ta ƙasa ta damƙe katan ɗin kwayar turamol guda 1,387 a cikin wasu kayayyaki a jihar Rivers, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Muna Neman Gwamnan Kaduna Ruwa a Jallo, Duk Wanda Ya Kamo Shi Akwai Tukuici, Inji NLC
Mrs Ifeoma Ojukwu, kakakin runduna ta 2 dake tashar jirgin ruwan Onne jihar Rivers, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Patakwal.
Ojukwu yace sun samu nasarar cafke ƙwayoyin ne da taimakon wasu takwarorin su na ƙasashen waje, kamar yadda thisday live ta ruwaito
Yace: "Mun kama kwayoyin ne cikin wasu kwantenoni dake ɗaukar 120mg, an zuba ƙaramin fakitin turamol ɗin guda 20 a cikin kowacce kwantena."
"Sannan mun sami wasu kwayoyin turamol ɗin a cikin katan ɗin tayils, inda aka yi amfani dashi wajen boye haramtattun kwayoyin."
KARANTA ANAN: Da Ɗumi Ɗumi: Ba Wani Sabon Bashi Shugaba Buhari Zai Karɓo Ba, Majalisa Tayi Ƙarin Haske
"Gaba ɗaya mun ƙwace kwayoyin turamon katan 1,387 tare da katan 1,000 na tayils ɗin da ake yin ciminti da shi."
"Mun samu nasarar damƙe waɗannan kwayoyin ne biyo bayan bibiya da mukayi har muka samu bayanai daga yan uwanmu na kasashen waje." inji shi.
Ya kuma ƙara da cewa suna cigaba da bincike dan gano wanda ke safararsu, da duk waɗanda ke da hannu a shigo da kwayoyin.
Yace jami'an zasu cigaba da gudanar da binciken ƙwaƙwaf akan duk kayan da ake safarar su ta yankin, Saboda haka duk wani mai aiki irin wannan ya kwana da shirin cewa boye kwayoyi a cikin halastattun kaya ba shine zaisa ya cimma nasara cikin sauki ba.
A wani labarin kuma Matsalar Tsaro: Zamu Yi Amfani da Dukkan Ƙarfin Mu Wajen Taimaka Wa Najeriya, Shugaban Faransa
Gwamnatin ƙasar Faransa tayi alƙawarin taimakawa Najeriya iya karfinta domin magance matsalar tsaron dake addabar ƙasar.
Shugaba Emmanuel Macron ne ya bayyana haka a wajen taron ƙasashen Africa dake gudana a Faris.
Asali: Legit.ng