Matsalar Tsaro: Zamu Yi Amfani da Dukkan Ƙarfin Mu Wajen Taimaka Wa Najeriya, Shugaban Faransa
- Gwamnatin ƙasar Faransa tayi alƙawarin taimakawa Najeriya iya karfinta domin magance matsalar tsaron dake addabar ƙasar
- Shugaba Emmanuel Macron ne ya bayyana haka a wajen taron ƙasashen Africa dake gudana a Faris
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa na maraba da Faransa da duk wata ƙasa dake shirin taimakawa a dawo da zaman lafiya a Najeriya
Ƙasar Faransa tayi alƙawarin taimka wa Najeriya wajen magance matsalar tsaron dake addabarta, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Rundunar Soji Ta Riƙe Albashin Sojoji 45 a Jihar Borno Saboda Wani Zargi
Babban mai taimakawa shugaban ƙasa Buhari wajen yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar.
Yace shugaba Buhari ya samu yardar shugaba Emmanuel Macron da gwamnatinsa a wajen taron ƙasashen Africa dake gudana a Faransa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
A jawabin, shugaba Macron yace gwamnatinsa na fatan taimakawa Najeriya da dukkan ƙarfinta domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasar ke fama dashi.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu
Jawabin yace: "Yayin jawabinsa a wajen taron, shugaba Macron ya nuna goyon bayansa ga Najeriya da jama'ar dake cikinta bisa namijin ƙoƙarin da suke yi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaron dake addabar su."
"Macron yace gwamnatinsa zata kawo ɗauki, zata yi amfani da duk ƙarfinta domin taimakawa ƙasar ta magance matsalar tsaron da yaƙi ci yaƙi cinyewa."
Shugaban Faranca ya ƙara da cewa gwamnatin sa zata taimakawa Najeriya wajen fuskantar ƙalubalen dake tattare da allurar rigakafin COVID19.
Shugaba Buhari ya tabbatar wa takwaransa na Faranca cewa Najeriya a shirye take tayi aiki tare da Faransa da sauran ƙasashen duniya domin tabbatar da an dawo da zaman lafiya a Najeriya.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China
Wasu yan bindiga sun kai sabon hari ƙauyen Nasko dake ƙaramar hukumar Magama a jihar Neja.
Jami'an soji sun maida martani ga yan bindigan inda akai ɗauki ba daɗi a tsakaninsu, biyu daga cikin sojojin sun rasa rayuwarsu.
Asali: Legit.ng