Da Ɗuminsa: Muna Neman Gwamnan Kaduna Ruwa a Jallo, Duk Wanda Ya Kamo Shi Akwai Tukuici, Inji NLC
- Ƙungiyar ƙwadugo NLC ta bayyana cewa tana neman Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-rufa'i ruwa a jallo
- Ƙungiyar tace ta shirya tsaf zata gurfanar da gwamnan a gaban shari'a bisa laifin korar ma'aikata ba bisa ka'ida ba
- Ana cigaba da musayar yawu tsakanin gwamnatin Kaduna da kuma ƙungiyar NLC tun bayan shigar NLC yajin aikin gargaɗi a jihar
Ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa NLC tace tana neman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ruwa a jallo, kamar yadda BBC ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi Ɗumi: Ba Wani Sabon Bashi Shugaba Buhari Zai Karɓo Ba, Majalisa Tayi Ƙarin Haske
Ƙungiyar ta kuma bada umarnin duk wanda ya ganshi to ya kama shi, zata bashi tukuici mai gwaɓi.
A baya dai, gwamnan Kaduna ya bayyana a shafinsa na tuwita @elrufai cewa yana neman shugaban NLC na ƙasa, Ayuba Waba, ruwa a jallo bisa zarginsa da aikata laifin karya tattalin arziƙi da gangan.
Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa gwamnan yace shugaban NLC da tawagarsa sun aikata laifi ƙarƙashin kundin laifuka na ƙasa kuma zasu kamo shi su gurfanar da shi.
KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Zamu Yi Amfani da Dukkan Ƙarfin Mu Wajen Taimaka Wa Najeriya, Shugaban Faransa
Ana ta wannan kace-nace tsakanin gwamnan da NLC tun bayan da NLC ta tsunduma yajin aikin gargaɗi a jihar tare da zanga-zanga.
Mai magana da yawun NLC ta ƙasa, Nasir Kabir, ya bayyana cewa ƙungiyar ta yanke shawarar shiga yajin aiki a ƙasa baki ɗaya daga ranar Litinin mai zuwa.
Yace ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne bayan da aka tura yan ta'adda su tarwatsa mambobin ƙungiyar da suka fito neman yancin su ranar Talata.
Yace: "Bayan wasu yan daba sun kaiwa mambobin mu hari da nufin tarwatsa su, ƙungiya ta ƙasa ta kira taron gaggawa, inda ana tsaka da taron ne muka samu labarin gwamnan Kaduna ya canza wa shugaban NLC na jihar wuri zuwa Birnin Gwari."
"Hakanan kuma muka sami labarin gwamnan ya sallami ma'aikatan jinya yan ƙasa da mataki na 14, da kuma maganar da yayi da yan Jarida cewa yana neman mu."
"Muna kira ga jama'a da jami'an tsaro su sanar damu da zarar sunga El-Rufa'i, sannan muna buƙatar su kamo shi domin ya fuskanci shari'a saboda matakin da ya ɗauka na sallamar ma'aikata ba bisa ƙa'ida ba."
A wani labarin kuma Rundunar Soji Ta Riƙe Albashin Sojoji 45 a Jihar Borno Saboda Wani Zargi
Rundunar Soji a jihar Borno ta riƙe albashin jami'anta guda 45 sabida tana zarginsu da ƙaurace wa wurin aiki.
Rundunar tace bayan ɗauke sojojin daga Marte, jami'an da abun ya shafa sun ɗauki hutu ba tare da sun nemi izini ba.
Asali: Legit.ng