'Yan Bindiga Sunyi Kisa, Sun Kuma Sace Mutum 21 a Sabon Harin da Suka Kai a Katsina
- Yan bindiga sun afka wa mutane a karamar hukumar Batsari sun sace mutane 21 ciki har da mata da yara
- Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da afkuwar harin inda ya ce sun kuma sace dabobi, wayoyin salula da wasu kayayyakin
- Amma kawo yanzu rundunar yan sandan jihar Katsina bata tabbatar da sace mutanen ba don ba a yi nasarar ji ta bakin kakakin yan sanda ba
An halaka mutum daya yayin da aka sace wasu mutane 21 mafi yawancinsu mata da yara a karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, The Channels ta ruwaito.
Wani da abin ya faru a idonsa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan bindihan sun kutsa garin na Batsari misalin 10.20 na dare suna ta harbe-harbe daga baya suka sace mutum 12.
DUBA WANNAN: Dogo Gide Ya Kashe 12 Cikin Yaransa Kan Rikicin Rabon Kayan Sata a Niger
Batsari na daya daga cikin kananan hukumomin da ke da iyaka da dajin Rugu inda ake samun karuwar hare-haren yan bindiga da masu satar shanu da garkuwa a jihar.
Ganau din ya ce bayan yan bindigan sun gama sace shanu, kayan mutane, wayoyin salla da miliyoyin naira sun halaka wani dan gudun hijira mai suna Alhaji Hassan dan asalin kauyen Zabuwa.
A halin yanzu rundunar yan sandan jihar Katsina bata tabbatar da afkuwar lamarin ba sakamakon rashin amsa waya da kakakin yan sandan jihar Gambo Isah bai yi ba a lokacin hada wannan rahoton.
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Halaka Direba Sannan Suka Sace Fasinjoji 13 a Nasarawa
A baya, rundunar yan sandan ta tabbatar da sace wani alkalin kotun shari'a a kauyen Baure Zaka da ke karamar hukumar Safara a jihar.
A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.
An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.
Asali: Legit.ng