Yajin Aikin Kaduna: 'Zo Ka Kama Ni Idan Zaka Iya,' Wabba Ya Faɗawa El-Rufai

Yajin Aikin Kaduna: 'Zo Ka Kama Ni Idan Zaka Iya,' Wabba Ya Faɗawa El-Rufai

- Shugaban kungiyar kwadago na kasa, NLC, Ayuba Wabba ya fadawa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya kama shi idan zai iya

- Hakan na zuwa ne gwamnan bayan gwamnan ya ayyana Wabba da wasu shugabannin NLC a matsayin wadanda ya ke nema ruwa a jallo

- Kungiyar ta NLC ta shiga yajin aikin ne kan korar ma'aikata da gwamnatin Kaduna ke yi da kuma rashin biyansu kudadensu bayan korar

Shugaban kungiyar kwadago na kasa, NLC, Ayuba Wabba ya fadawa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ya ce yana nemansa ruwa a jallo ya kama shi idan ya isa saboda yajin aikin da ake yi a jihar.

Shugaban na NLC ya ce, "gwamnan ya zo ya kama ni" a yayin da ya ke jagorantar zanga-zangar lumana a babban birnin jihar ta Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Dahiru Bauchi Ya Amince Da Sanusi A Matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya

Yajin Aikin Kaduna: 'Zo Ka Kama Ni,' Wabba Ya Fadawa El-Rufai
Yajin Aikin Kaduna: 'Zo Ka Kama Ni,' Wabba Ya Fadawa El-Rufai. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

A gajeren hirarda aka yi da shi a shataletalen NEPA yayin da ya ke jagorantar dubban ma'aikata zin zanga-zangan, Wabba ya ce, "ba don ni ake yajin aikin ba."

"Ya zo ya kama ni. Muna nan muna jiran su." a cewar Wabba.

Tunda farko, Gwamna Nasir El-Rufai ya ayyana cewa yana neman shugaban na NLC Ayuba Wabba ruwa a jallo kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: An Rushe Tashar Mota Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja

Ana nemansa ruwa a jallo ne saboda yunkurin gurgunta tattalin arziki da hari kan kayayyakin gwamnati a karkashin dokar Miscellaneous Offences Act.

A ranar Litinin, Wabba ya sha alwashin sai ya gurgunta gwamnatin Mallam Nasiru El-Rufai har sai ya dawo da ma'aikatan da ya sallama daga aiki.

Shi kuma gwamnan a bangarensa ya ce babu ja da baya kan batun sallamar ma'aikatn da gwamnatinsa ta fara.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164