Fashewar Gas Na Bogi Ya Kashe Mutane 2, Wasu Sun Jikkata a Wani Otal

Fashewar Gas Na Bogi Ya Kashe Mutane 2, Wasu Sun Jikkata a Wani Otal

- Ana zargin fashewar gas na bogi ya hallaka mutane biyu a otal din wani tsohon gwamnan Ogun

- Hakazalika wasu mutane uku sun ji raunuka daban-daban a yayin da gas din ya fashe a bakin kofa

- Rahotanni sun bayyana cewa, gas din ya fashe ne yayin da ake kokarin gyara kofar mashiga otal din

Kasa da mako guda bayan fashewar gas a Abeokuta, wata fashewar ta sake faruwa a ranar Litinin a Abeokuta, jihar Ogun, inda mutane biyu suka mutu wasu uku suka ji rauni.

Lamarin wanda ya faru a otal mallakin tsohon gwamna Gbenga Daniel, an ruwaito cewa ya faru ne da misalin karfe 12 na dare lokacin da wani ma'aikaci ke cika wata kofa mai sarrafa kanta a kofar otal din.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa wani ma'aikaci da kuma daya da ake zaton yana daya daga cikin ma'aikatan sun mutu nan take, yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC Ke Kitsa Dukkan Kone-Konen Ofisoshin INEC a Fadin Kasar Nan, Inji PDP

Fashewar Gas Na Bogi Ya Kashe Mutane 2, Wasu Sun Jikkata a Wani Otal
Fashewar Gas Na Bogi Ya Kashe Mutane 2, Wasu Sun Jikkata a Wani Otal Hoto: conferencehotelnigeria.com
Asali: UGC

An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin tarayya dake Idi-Aba, Abeokuta, yayin da aka ajiye ragowar wadanda suka mutu a dakin aje gawarwaki na babban asibitin da ke Abeokuta.

Da yake bada bayani, manajan otal din, Engr. Tunde Osinubi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa yi yi nadamar faruwar lamarin matuka, The Nation ta ruwaito.

Osinubu, a cikin wata sanarwa, ya danganta abin da ya fashe a Hotel din da "silindan iska na bogi."

Ya ce: “Ana gudanar da aikin gyaran kofar mai sarrafa kanta a kofar karbar baki na otal din, wanda ya hada da amfani da iskar gas ta oxyacetylene wajen murda marfin kofofin.

“Silindan gas din Oxyacetylene ya fashe ba zato ba tsammani, ya kashe mai gyaran da wani mutum guda a har yanzu ba a gano shi waye ba.

“Fannin gudanarwa ba otal din na jajantawa wa iyalai da abokan mamatan kuma suna yi wa jama’a gargadi game da kasancewar bazuwar na bogi gas a cikin kasuwa."

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

A wani labarin, Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) ta shawarci ’yan Najeriya kan yadda za su kauce wa fadawa cikin matsalar mulkin mallaka na zamani, jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumar NITDA ta shawarci masu amfani da shafukan sada zumunta, musamman WhatsApp da su guji musayar bayanansu na sirri a wadannan shafuka.

Hukumar ya yi gargadin cewa cewa wa'adin farko (na wadannan dandamali) na sirri da tsaro yanzu haka an mamaye su bisa tushen fifita kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel