Rundunar Soji Ta Riƙe Albashin Sojoji 45 a Jihar Borno Saboda Wani Zargi
- Rundunar Soji a jihar Borno ta riƙe albashin jami'anta guda 45 sabida tana zarginsu da ƙaurace wa wurin aiki
- Rundunar tace bayan ɗauke sojojin daga Marte, jami'an da abun ya shafa sun ɗauki hutu ba tare da sun nemi izini ba
- Amma ɗaya daga cikin sojojin da abun ya shafa yace sam zargin da ake musu ba gaskiya bane
Hukumomin soji a Maiduguri sun riƙe albashin jami'an su guda 45 saboda suna zargin su da aikata ba dai-dai, kamar yadda wata majiya ta faɗawa Dailytrust.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu
Sojojin da abun ya shafa suna daga cikin bataliya ta 153 waɗanda aka ɗauke daga garin Marte, jihar Birno bayan kwashe shekara uku suna yaƙi da yan ta'adda.
Rundunar sojin na zarginsu da saɓawa dokar aikin soja.
Yan ta'adda sun kaiwa wannan bataliyar sojojin hari har sau uku, wanda yayi sanadiyyar kashe sojoji da dama yayin da makamai, kayan aiki da motocin yaƙi suka salwanta.
Amma rundunar soji tayi gaggawar ɗauke bataliyar daga Marte bayan an kai musu hari na uku a watan Fabrairu.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China
Wata majiya ta bayyana cewa rundunar soji tayi gaggawar yin canje-canje a cikin bataliyar, inda aka ɗauke wasu sojoji aka canza musu wurin aiki a Maiduguri.
"Wasu daga cikin sojin da aka canzawa wurin aiki sun daina zuwa inda aka tura su, ana zargin sun ɗauki hutu ne ba tare da neman izini ba. A dalilin haka albashin su na watan Afrilu ya maƙale." inji majiyar.
Amma ɗaya daga cikin sojin da abun ya shafa yace zargin da ake musu na ƙauracewa wurin aiki ba gaskiya bane.
"Ba'a biya mu albashin mu ba, da muka tuntuɓi masu kula damu kan lamarin, sun ce mana an riƙe albashin mu ne saboda mun daina zuwa wurin aiki, hakan ya matukar bamu mamaki." inji sojan.
Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a kan wannan labarin:
Ashiru Hamza:
"Ya kamata dai a hanzarta wurin binciken domin gano gaskiar abinda ake zargin su, idan basu da laifi asakar masu da kudin su idan kuma suna da laifi sai a hukunta su kamar yadda doka ta tanada."
Mustafah Abubakar:
"Miye dalilin su nayin haka ya kamata ayi bincike"
Sir Suraj Bungudu:
"Buhari yayi Allah wadai"
A wani labarin kuma Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000
Rahotanni sun bayyana cewa an damke wani na kusa da gwamnan jihar Ogun a ƙasar Amurka bisa zarginsa da satar wasu kuɗaɗe.
An bayyana cewa Abidemi Rufa'i, babban mai taimakawa gwamnan, ya shiga hannu ne a ranar jumu'a da yamma.
Asali: Legit.ng