Jam'iyyar APC Ke Kitsa Dukkan Kone-Konen Ofisoshin INEC a Fadin Kasar Nan, Inji PDP

Jam'iyyar APC Ke Kitsa Dukkan Kone-Konen Ofisoshin INEC a Fadin Kasar Nan, Inji PDP

- JAam'iyyar PDP ta zargi APC da alhakin kone ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC)

- PDP ta ce gwamnatin APC na kone-konen ne saboda wani makirci da take dashi a boye a 2023

- Ba wannan bane karo na farko da PDP ta zargi gwamnatin jam'iyyar APC da aikata irin wannan

Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da laifin kona ofisoshin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da aka yi kwanan nan a kasar.

Jam’iyyar adawar ta yi zargin cewa APC ce ke da alhakin tada hargitsi saboda tana aiki kan samar da wani yanayi na gaggawa don dakile zabuka masu zuwa ganin cewa ba za ta iya cin zabe a kasar ba.

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Kola Ologbondiyan wanda ya yi wannan zargin a wani taron manema labarai ya ce ya damu da shirun da APC tayi yayin kone-kone da lalata kayan aikin INEC, Leadership ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje Za Ta Kara Daukar Likitoci Aiki a Jihar Kano

Jam'iyyar APC Ke Kitsa Dukkan Kone-Konen Ofisoshin INEC, Inji PDP
Jam'iyyar APC Ke Kitsa Dukkan Kone-Konen Ofisoshin INEC, Inji PDP Hoto: newsbreakng.com
Asali: UGC

Da yake amsa tambaya kan kona ofisoshin na INEC, ya ce, “Yayin da muka kusanci zaben 2023, muna cikin damuwa a matsayinmu na jam’iyya cewa APC da ke jagorantar gwamnatin tarayya ta yi shiru duk da irin kone-kone da ake yi a ofisoshin INEC.

“Kuma muna da shakkun cewa APC ta gaza wa 'yan Najeriya kuma fahimtar cewa ba za ta iya cin zabe a gaba ba ne ke da alhakin wannan rudanin, saboda suna aiki kan samar da wani yanayi na gaggawa don dakile zabubbuka masu zuwa.

“Idan INEC ba ta da sauran kayan da za ta gudanar da zabe, ta yaya za a gudanar da zaben. Ta yaya za'a tabbatar da dimokuradiyyar mu.

"Jam’iyyar PDP ta damu matuka da cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC ta yi shiru, alhali kuwa a kalla ofisoshin INEC 20 suka kone,” inji shi.

A shekarar 2020, jam'iyyar PDP ta jihar Imo ta yi irin wannan zargi biyo bayan konewar ofishin INEC na jihar a ranar Lahadi, 2 ga watan Fabrairun 2020, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Ta zargi jam'iyyar APC da alhakin kone ofishin hukumar ta zabe mai zaman ta kasa, a cewarta saboda "ta shirya ta sake yin duba ga hukuncin da ta yanke a kan zaben gwamnan Imo na 2019."

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: An Dawo da £4.2m Zuwa Najeriya, Kudaden Da Ibori Ya Sace

A wani labarin, Gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya aika da kudirin zartarwa ga majalisun dokokin kasa don yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki ta yadda za a yi karin iko ga jihohi.

Kungiyar gwamnonin na PDP sun yi taro a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Litinin don tattaunawa kan halin da kasa ke ciki, matsalar rashin tsaro, da tattalin arziki, The Cable ta ruwaito.

A karshen taron, sun fitar da sanarwa da ke dauke da kudurin nasu, in da wani yankin sanarwar ke kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya "gaggauta aika kudirin doka ga Majalisar Dokoki ta kasa don yin kwaskwarima ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel