Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu

Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu

- Sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, ya ƙaddamar da rundunar 'Operation dawo da zaman lafiya' a jihar Enugu

- Ana fatan wannan sabuwar rundunar zata magance yawan hare-haren da ake kaiwa yankin musamman a kan kayan gwamnati

- Wannan na zuwa ne kwana biyu da wasu yan bindiga suka kai hari hedkwatar INEC dake jihar Enugu

Sufeta janar na yan sanda (IGP), Usman Alƙali Baba, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar yan sanda da akai wa take 'Operation dawo da zaman lafiya' a jihar Enugu kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China

Sabuwar rundunar zata yi yaƙi ne a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan domin dawo da cikakken zaman lafiya a yankin.

An gudanar da taron ƙaddamar da rundunar yau Talata a Micheal Okpara Square dake birnin Enugu, babban birnin jihar ta Enugu.

Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu
Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu Hoto: @policeNG
Asali: Twitter

Daga cikin waɗanda suka halarci taron kaddamarwan akwai gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne kwana biyu kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari Hedkwatar hukumar zaɓe INEC a jihar Enugu, inda suka ƙona motoci da wasu kayayyaki ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: Ka Miƙa Kanka Ofishin Yan Sanda Dake Kusa, El-Rufa’i Ga Shugaban NLC

Rahoto ya bayyana cewa yan bindigan sun ƙona motoci shida a harin da suka kai ofishin INEC ɗin na jihar Enugu.

Hakanan kuma a watan Afrilu, yan bindiga sun kashe jami'an yan sanda biyu a harin da suka kai ofishin Adani, karamar hukumar Uzo-Uwani jihar Enugu.

Irin waɗannan hare-haren sun jefa mutane cikin damuwa game da zaman lafiya a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

A wani labarin kuma Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000

Rahotanni sun bayyana cewa an damke wani na kusa da gwamnan jihar Ogun a ƙasar Amurka bisa zarginsa da satar wasu kuɗaɗe.

An bayyana cewa Abidemi Rufa'i, babban mai taimakawa gwamnan, ya shiga hannu ne a ranar jumu'a da yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel