Da duminsa: Gwamna Abiodun ya sallami hadiminsa da aka kama a Amurka kan zambar $350,000

Da duminsa: Gwamna Abiodun ya sallami hadiminsa da aka kama a Amurka kan zambar $350,000

- Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya dakatar da Abidemi Rufai

- Gwamnatin Amurka ta kama Rufai, wanda ya kasance babban hadimi na musamman ga Abiodun kan ayyuka na musamman bisa zargin zamba

- Sai dai gwamnan, ya ce ba za a iya kama shi da laifin abin da Rufa'i ya aikata ba

Sa’o’i kadan bayan gwamnatin Amurka ta kama shi, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya dakatar da babban mataimakinsa na musamman a kan ayyuka na musamman, Abidemi Rufai.

Ofishin Bincike na FBI ya kama Rufa’i a birnin New York kan zarginsa da hannu a damfarar dala 350,000 na tallafin marasa aikin yi a ƙasar.

KU KARANTA KUMA: Yajin aikin Kaduna: Ka sasanta da kungiyar kwadago, gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai

Da duminsa: Gwamna Abiodun ya sallami hadiminsa da aka kama a Amurka kan zambar $350,000
Da duminsa: Gwamna Abiodun ya sallami hadiminsa da aka kama a Amurka kan zambar $350,000 Hoto: Abidemi Rufai.
Asali: Facebook

Yayinda yake maida martani ta bakin babban sakataren yada labaransa, Kunle Somorin, gwamna Abiodun ya ce labarin kasancewar hadiminsa da hannu a cikin zamba abun damuwa ne, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sai dai gwamnan, ya ce ba za a ɗora masa alhakin abubuwan da babban mutum mai hankali ya aikata ba.

Ya ce:

"Mun samu labari mai matukar tayar da hankali game da kame daya daga cikin masu rike da mukaman siyasa na gwamnan, Mista Abidemi Rufai a New York kan zargin zamba a Amurka, da safiyar yau."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar NLC da ke gudana a Kaduna

PM News ta ruwaito cewa Abiodun ya kuma yi Allah wadai da duk wani abu da zai kawo nakasu ga kudirinsa na kirkirar gaskiya, rikon amana a jihar da kuma cikin shugabanci.

Ya kara da cewa har yanzu yana nan kan bakansa na gina makomar jihar, yana mai cewa ba zai lamunci masu laifi ba a gwamnatinsa ko a jihar baki daya.

A baya mun ji cewa Ƙasar Amurka ta cafke babban mai taimakawa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da zargin sama da faɗi da dala dubu $350,000 na tallafin marasa aikin yi a ƙasar.

An damƙe Abidemi Rufa'i ranar Jumu'a da yamma a filin tashi da saukar jiragen sama JFK dake birnin New York, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A jawabin ofishin Antoni Janar na Amurka a Washinton, ya bayyana cewa an shigar da ƙorafi ne a kan Rufa'i da zargin ya sace dala dubu $350,000 kuɗin tallafawa marasa aikin yi daga sashin ɗaukar aiki ESD dake Washinton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel