Ka Miƙa Kanka Ofishin Yan Sanda Dake Kusa, El-Rufa’i Ga Shugaban NLC

Ka Miƙa Kanka Ofishin Yan Sanda Dake Kusa, El-Rufa’i Ga Shugaban NLC

- Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i yayi kira ga shugaban NLC ya miƙa kansa ofishin yan sanda mafi kusa dashi

- Gwamnan ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani taro da ya halarta

- Yace NLC sun tafka babban laifi ƙarƙashin laifukan da ake hukunci akansu, kuma ya kamata a kama shugaban su

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya dage a kan cewa sai an damƙe shugaban ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa NLC, Ayuba Waba, bisa laifin ƙoƙarin karya tattalin arziƙi.

KARANTA ANAN: Amurka Ta Damƙe Wani Nakusa da Gwamnan Ogun Bisa Zargin Sace Dala Dubu $350,000

Gwamnan ya kira yi Ayuba Waba ya miƙa kansa ofishin yan sanda mafi kusa dashi domin a gurfanar dashi, kamar yadda The nation ta ruwaito.

El-Rufa'i yace shugaban NLC ɗin ya karya dokar da ya kamata a hukunta shi ƙarƙashin kundin dokokin ƙasa.

Tunda safiyar yau Talata ne, gwamnan Kaduna ya bayyana shugaban NLC, Ayuba Waba, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a shafinsa na Tuwita @elrufai.

Ka Miƙa Kanka Ofishin Yan Sanda Dake Kusa, El-Rufa’i Ga Shugaban NLC
Ka Miƙa Kanka Ofishin Yan Sanda Dake Kusa, El-Rufa’i Ga Shugaban NLC Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Yace babu gudu babu ja da baya a kan matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na korar wasu ma'aikata, kuma yace jihar sa bata shirya yin jayaayya da NLC ba.

Gwamnan wanda ya amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kaddamar da sabon tsarin inganta harkar Noma, wanda ma'aikatar noma ta jihar ta shirya, yace ƙungiyar kwadugo ta tafka laifin karya tattalin arziƙi kuma ya kamata a kama shugabanta.

Sai dai har zuwa yanzun gwamnatin Kaduna bata kama shugaban NLC ɗin ba kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Twitter Ta Zaɓi Najeriya Domin Gwada Sabon Salon Sakonta Na Murya

Gwamnan yace:

"Eh, nayi rubutu a shafina na tuwita, mambobin ƙungiyar sun kai hari wasu wuraren gwamnati, sannan suna ƙoƙarin karya tattalin arziƙin mu da gangan, wannan laifi ne karkashin laifukan da ake hukunci a kansu."

"Yanzu haka muna nemansa (shugaban NLC), ya miƙa kansa ofishin yan sanda mafi kusa dashi ko ya kawo kansa garemu, zai fuskanci hukunci dai-dai da laifin da ya aikata."

Da aka tambayi gwamnan ko akwai saɓani a tsakaninsu, sai yace: "Ba dalilin da zaisa muyi jayayya da su, sun ɗauki matakin da shi kaɗai zasu iya ɗauka kuma hakan bazai canza komai ba."

A wani labarin kuma CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba

Ƙungiyar CAN ta goyi bayan shawarar da tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, ya baiwa gwamnati kan matsalar tsaro.

IBB ya shawarci gwamnatin tarayya data siyo sabbin makamai na zamani sannan ta horad da jami'an tsaro yadda zasu yi amfani da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel