Daiɗaita NPA kika je yi ba cigaba ya kai ki ba, Hadiza Bala Usman ga Binta Garba

Daiɗaita NPA kika je yi ba cigaba ya kai ki ba, Hadiza Bala Usman ga Binta Garba

- Hadiza Bala usman ta caccaki Sanata Binta Garba a kan zargin da ta jefe ta dashi bayan dakatar da ita da aka yi

- Kamar yadda tsohuwar shugaban NPA din tace, dama can Sanata Binta taje hukumar ne da burin daidaita ta ba kawo cigaba ba

- Bala Usman tace a lokacin da Garba ke hukumar me ya hanata fitar da dukkan zargin ba sai bayan da ta bar wurin ba

Dakatacciyar shugaban hukumar NPA, Hadiza Bala Usman ta yi martani da tsohuwar mamba a hukumar, Sanata Binta Garba wacce ta zargeta da waddaka da kudaden hukumar.

Garba ta zargi Usman da assasa korarta daga hukumar NPA a kan yadda ta nuna rashin amincewarta da rahotannin shige da ficen kudade.

A yayin martani, dakatacciyar shugaban NPA a wata takarda da ta sa hannu a ranar Litinin, ta musanta zargin da Garba ke yi mata inda tace Sanatan ta je hukumar ne domin daidaita ta ba wai kawo cigaba ba.

KU KARANTA: Jarumi Lawan Ahmad ya zabgawa jaruma mai tasowa mugun mari a wurin shirya fim

Daiɗaita NPA kika je yi ba cigaba ya kai ki ba, Hadiza Bala Usman ga Binta Garba
Daiɗaita NPA kika je yi ba cigaba ya kai ki ba, Hadiza Bala Usman ga Binta Garba. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

Kamar yadda wani sashi na takardar ta sanar, "Baya ga cewa Sanata Binta bata fadi wani abu mai muhimmanci ba, ta tsaya ne tana fadin zargi marasa tushe a takardar da ta fitar ta ranar Lahadi, ta bada kanta inda ta nuna cewa ta shiga hukumar NPA ne domin kawai daidaicewa a maimakon kawo cigaba.

"Kamar yadda nace, ta dogara ne da zargin cewa ta jajirce a kan yadda kudi ke shiga da fita NPA wanda duk karya ne, cike da kwarin guiwa tun daga 2016 na sanar da cewa NPA na shirye domin karbar kowanne irin kalubale daga jama'a."

A yayin bayani kai tsaye, Usman tace hukumar karkashin mulkinta ta dauka matakai masu yawa wurin tabbatar da cewa komai a bayyane yake a hukumar.

KU KARANTA: Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa

A don haka Usman ta kalubanci ikirarin sanatan inda tace me yasa a lokacin bata rubuta takarda ba domin kalubalantar ta.

Ta ce: "A don haka akwai wasu tambayoyi da ya dace sanatan ta amsa: A lokacin da masu kididdige shige da ficen kudi suka gabatarwa kwamitin kudi rahoto kuma tana mamba, me yasa bata nemi karin bayani ba?

"Idan kuma ta nema me ya faru? Da bata gamsu da tambayoyin da tayi ba me ya hana ta rubuta koke ko korafi? Me yasa sai a halin yanzu take maganar?"

A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce "dukkan 'yan Najeriya" ne suke bukatarsa da ya nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A yayin jawabi a ranar Juma'a yayin da ake yin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai bada ansa ga wannan bukatar nan babu dadewa.

Gwamnan yace 'yan Najeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng