Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya alanta neman shugaban NLC, Ayuba Waba, ruwa a jallo

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya alanta neman shugaban NLC, Ayuba Waba, ruwa a jallo

- Yajin aikin da kungiyar NLC ta shirya a Kaduna ya shiga kwana na biyu

- An kulle gidajen mai, bankuna, tashohiin jirgin sama da kasa, dss

- Gwamnatin Kaduna ta ce wannan fito-na-fito ne ga tattalin arzikin jihar

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya alanta neman shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Kwamred Ayuba Wabba, da sauran shugabannin da suka shiga jihar zanga-zanga ruwa a jallo.

El-Rufa'i ya yi alkawarin bayar da kyautar kudi ga duk wanda ya san inda wadannan shugabannin kwadago suke boye.

Ya tuhumcesu ne da laifin fito-na-fito da tattalin arzikin jihar Kaduna kuma hakan ya sabawa doka.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita.

"Ana neman Ayuba Wabba da sauran shugabannin NLC ruwa a jallo bisa laifin fito-na-fito na tattalin arziki da dukiyar Kaduna karkashin dokar kananan laifuka," El-Rufa'i yace.

"Duk wanda ya san inda yake boye ya aikewa ma'aikatar Shari'a sako. Za'a bada babban kyauta."

KU KARANTA: A shekara 6, sai da Gwamna El-Rufai ya sallami ma’aikata 60,000 daga aiki – Falana, ASCAB

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya alanta neman shugaban NLC, Ayuba Waba, ruwa a jallo
Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya alanta neman shugaban NLC, Ayuba Waba, ruwa a jallo Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yajin aiki: Kuyi hakuri ku dagawa El-Rufa'i kafa, Kungiyar Gwamnoni ta roki NLC

Kungiyar kwadago Najeriya NLC a ranar Litinin ta kaddamar da yajin aiki kare dangi na kwanaki 5 a jihar Kaduna kan yunkurin da gwamnatin jihar keyi na korar dubban ma'aikata.

Yan kwadagon sun gudanar da zanga-zanga inda suka lashi takobin durkusar da jihar har sai gwamnatin jihar ta amsa bukatunsu.

Sakamakon haka an rufe ma'aikatun gwamnati, bankuna, tashohon jirgin sama da na kasa, gidajen mai, da kuma kamfanonin wutan lantarki.

Shi kuma gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, ya lashi takobin cewa ba zai sauraresu ba.

A ranar Asabar El-Rufai yace gwamnatinsa ba za ta saurari kowanne irin bacin suna ba, tare da jaddada cewa ba zai yuwu ya kashe kashi 84 zuwa 96 na kudin da yake samu daga gwamnatin tarayya ba zuwa biyan albashi.

Gwamnatin jihar tace ana ta gangamin shirya mata karairayi da ikirari marasa tushe inda aka ce ta sallama ma'aikata 4000 kuma ta daina biyan sabon mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng