Twitter Ta Zaɓi Najeriya Domin Gwada Sabon Salon Sakonta Na Murya
- Kamfanin Tuwita ya zaɓi Najeriya a matsayan ɗaya daga cikin ƙasar da za'a fara amfani da sabon tsarin tura saƙo ta hanyar naɗar murya
- Ana ganin dai Kamfanin ya zaɓi Najeriya ne saboda yawan mutanen dake amfani da dandalin sada zumuntar Tuwita
- Yace zai cigaba da inganta amfani da dandalinsa na Tuwita domin sauƙaƙa wa masu amfani da shi
A jiya ne Kamfanin sada zumunta na Tuwita ya ƙara sabon tsarin tura saƙon murya a dandalin, kuma ya zaɓi Najeriya da Turkey a matsayin kasashe biyu na farko da za'a yi gwajin farko.
KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: CAN Ta Goyi Bayan Shawarar Tsohon Shugaban Ƙasa IBB, Tace Wannan Ba Shine Karon Farko Ba
Ana ganin dai zaɓen da Kamfanin tuwita yayi wa Najeriya bazai rasa nasaba da yawan mutanen dake amfani da kafar sada zumuntar ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Anyi ƙiyasin sama da yan Najeriya miliyan bakwai ne ke amfani da tuwita, kuma wannan sabon tsarin zai bada damar tura saƙon murya har tsawon daƙiƙa 140.
Yayin da kamfanin ke jawabin dalilin samar da wannan tsarin, yace:
"Akwai abubuwa da yawa da ba za'a faɗa ba ta hanyar amfani da rubutu, saboda haka munason mutane su fara tattaunawa tsakaninsu kan abubuwan dake faruwa da su ta hanyar amafani da saƙon murya."
KARANTA ANAN: Daga Ƙarshe, Mataimakin Shugaban Ƙasa Osinbajo Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takara a 2023
"Mun ƙagu muga yadda za'a yi amfani da wannan sabon tsarin a waɗannan kasashe biyu, kuma muna jiran ra'ayoyin jama'a akan tsarin na saƙon murya."
"Dadandalin tuwita wuri ne da zakaje ka faɗi ra'ayinka akan abubuwan dake faruwa, a koda yaushe muna sauraron buƙatar masu amfani da tuwita kuma zamu cigaba da inganta dandalin domin sauƙaƙawa mutane amfani da shi."
Kamfanin ya cigaba da cewa: "Domin inganta fira a tsakanin mutane, mun ƙirƙiro tura saƙon murya wanda za'a fara amfani dashi a Turkey da Najeriya daga yau."
"Wannan zai baiwa mutane damar tura saƙon su cikin sauƙi, ko dai suna son tura muryar a lokacin ko kuma idan suna sauri."
A wani labarin Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6
Wasu yan bindiga sun kai hari hedkwatar hukumar zaɓe INEC ta jihar Enugu , inda suka ƙona Motocin Hilux shida dake harabar wajen.
Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar maharan waɗanda suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin ginin ofishin.
Asali: Legit.ng