Ku Tursasa 'Yan Boko Haram Su Mika Wuya, CDS Ga Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam

Ku Tursasa 'Yan Boko Haram Su Mika Wuya, CDS Ga Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam

- Babban hafsan hafsoshin tsaro ya nemi kungiyoyin kare hakkin dan adam su tilasta Boko Haram su tuba

- Ya bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen rage zubar da jini a yaki da ake da kungoyin ta'addanci

- Sai dai, kungiyoyin kare hakkin dan adam din sun ce ba ya daga cikin ayyukansu tunkarar 'yan ta'adda

Babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor, ya yi kira ga kungiyoyin kare hakkin dan adam da su matsawa 'yan kungiyar Boko Haram su ajiye makamansu su zo teburin tattaunawa daidai da yadda suke yi wa sojojin gwamnati da ke yaki da ta'addanci.

Sai dai, yayin da kungiyoyin kare hakkin dan adam ke cewa ba ya daga cikin aikinsu shiga cikin 'yan ta'adda, amma sun ba da shawarar a gudanar da ayyukan shawo kan ta'addanci ta hanyar leken asiri, The Guardian ta ruwaito.

A cewar Irabor, idan har masu rajin kare hakkin dan adam suka dauki gangamin kare hakkin dan adam ga kungiyoyin ta'addanci, za a magance rikicin cikin sauri tare da rage zubar da jini.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamnan Kwara da Zargin Karkatar da Kudi

Ku Tursasa 'Yan Boko Haram Su Mika Wuya, CDS Ga Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam
Ku Tursasa 'Yan Boko Haram Su Mika Wuya, CDS Ga Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Irabor ya yi magana ne a wajen bikin bude wani taron na kwanaki uku kan 'Shawarwarin Kwamitin Afirka kan 'Yancin Dan Adam a Ayyukan Yaki da Ta'addanci' wanda Cibiyar Bincike da Nazari (CSRS) ta Kwalejin Tsaro ta Kasa (NDC) ta shirya tare da kungiyar OSIWA.

Ya ce: “Abin da nake bukata na gabatar muku kuma, tabbas, da sauran masu ruwa da tsaki a cikin tsarin kare hakkin dan adam, shi ne cewa galibi kun gano cewa an fi matsawa ga sojojin gwamnati da ke magance ta’addanci.

Ya kuma bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin dan adam din kan ba da karfi "kadan ko kuma mai da hankali kadan ga 'yan ta'adda; Boko Haram da Daular Islama a Yammacin Afirka (ISWAP).”

Da take maida martani, Babbar Daraktar OSIWA, Aisha Osori, ta ce ba hurumin kungiyoyin kare hakkin dan adam bane matsa lamba kan ‘yan ta’adda ko tilasta su su mika wuya.

“Ba mu san 'yan ta’adda ba kuma su ma ba su san mu ba, don haka ba za mu iya matsa musu lamba ba.

"Wannan shine dalilin da ya sa muka ta'allaka nauyin kan rundunoninmu na yaki don kawar da wadanda suka dauki makami don yaki da kasa. Amma a yin haka, bai kamata mu kaskantar da kai zuwa matsayin 'yan ta'adda ba ta hanyar take hakkin dan adam."

“A Najeriya, an samu rahotanni na amfani da karfi fiye da kima da sojoji ke yi a duk fadin kasar. Tare da girke sojoji a jihohi 35 daga cikin 36 na tarayya, akwai matukar bukatar horas da sojoji kan ‘yancin dan adam,” inji ta.

Amma Babban Sakataren Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta Kasa (NHRC), Anthony Ojukwu, ya ba da shawarar aiwatar da ayyukan shawo kan ta'addanci na sirri wanda zai kare 'yan kasa marasa laifi daga mummunan yaki.

KU KARANTA: Gwamnoni 13 Na PDP Sun Shiga Taron Sirri Don Tattauna Matsalar Rashin Tsaro

A wani labarin, A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta ba da sanarwar cewa ta cafke wani dan sanda na bogi kuma dan bindiga, mai suna Michael Osundu.

A cewar kakakin rundunar, tare da Orlando Ikeokwu, an gano bindiga guda daya da harsasai 26, da kuma kakin ‘yan sanda guda biyu masu mukamin Mataimakin Sufeta Janar, wadanda aka boye su a cikin motarsa ​​kirar Toyota Escalade mai bakin gilashi.

Ikeokwu ya bayyana cewa ana zargin Osundu dan kungiyar 'yan daba ne da suka kai hari hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar da kuma gidan yari na Owerri a ranar 5 ga Afrilu, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel