Dahiru Bauchi Ya Amince Da Sanusi A Matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya

Dahiru Bauchi Ya Amince Da Sanusi A Matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya

- Sheikh Ɗahiru Bauchi ya amince da tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyya

- Shaihin ya taya Sanusi II murna ne yayin da ya tafi nuna masa wasikar naɗinsa a ranar Litinin a Bauchi

- Ɗahiru Bauchi ya ce wannan nadin tamkar Janar ne na Soja yana mai addu'ar Allah ya yi wa Sanusi II jagoranci

Babban malamin addinin musulunci, Shiekh Ɗahiru Usman Bauchi, ya amince da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya, yana mai masa addu'a Allah ya kiyaye shi ya masa jagoranci.

Malamin ya bayyana amincewarsa ne a ranar Litinin a lokacin da tsohon sarkin na Kano ya gabatar masa da wasikar naɗinsa a matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a Bauchi, rahoton Daily Trust.

Dahiru Bauchi Ya Amince Da Sanusi A Matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya
Dahiru Bauchi Ya Amince Da Sanusi A Matsayin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Sace Farfesa Da Mijinta a Gidansu

"Naɗin ka matsayin Khalifan Tijjaniyya tamkar Janar ne a Rundunar Sojoji kuma ko cikin Janar akwai manya. Muna maraba da naɗin ka a matsayin Khalifa kuma mun yaba da hangen nesan ka da girmama manya. Ina kira gare ka ka yi koyi da kakanka Muhammadu Sanusi I."

"Na yi murna dan zaɓen ka a matsayin jagora kuma ina maka addu'ar fatan Allah ya kiyaye ka ya yi maka jagora," in ji shi.

KU KARANTA: Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila

Shaihin ya shawarci Sanusi kada ya bari abokansa su yi tasiri game da sabon matsayinsa na jagorar ɗarikar, ya kara da cewa matsayi ne na addini wanda bai dace a haɗa shi da siyasa ko kasuwanci ba.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel