Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila

Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila

- Sojojin kasar Isra'ila sun ce an harbo musu roka har guda 3,150 daga yankin Falasdinawa cikin mako daya

- Amma Isra'ilan ta ce 460 cikin rokar ba su iso yankinta ba domin sun fadi sun fashe ne a yankin Zirin Gaza

- Isra'ila ta mayar da martani kan hare-haren da ake zargin Hamas da wasu kungiyoyi ke kaiwa amma a yanzu ba a tantance adadin roka da ta harba ba

Rundunar sojojin kasar Isra'ila, a safiyar ranar Litinin ta ce yan kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa sun harba roka 3,150 daga Zirin Gaza zuwa Isra'ila mako guda bayan rikici ya barke tsakaninsu, Daily Trust ta ruwaito.

Rundunar sojojin ta ce roka 460 ba su samu isowa yankin Isra'ila ba kuma sun fashe ne a yankin na Gaza.

Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila
Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Rushe Tashar Mota Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja

Garkuwar makaman roka ta Iron Dome da kasar Isra'ila ta mallaka na da nasarorin aiki na kashi 90 bisa dari wajen lalata makaman roka a tsakiyar sararin samaniya kafin su kai ga fadawa kan yankunan birane masu yawan mutane na Isra'ila.

iya dakile harin roka kashi 90 cikin 100 a cewa rundunar sojin.

Idan aka kwatanta da yakin Zirin Gaza da aka kwashe kwanaki 51 ana yi a 2014, roka 4,481 kungiyoyin kasar Falasdinu suka harba wa Isra'ila.

A halin yanzu babu kididdigan adadin hare-haren da kasar Isra'ila ta kai Zirin Gaza a cewar rundunar sojin na Isra'ila.

Kungiyoyin Falasdinawa da ke zirin Gaza ne suka fara harba roka ga kasar Isra'ila a kimanin mako daya da ta gabata a yammacin ranar Litinin.

KU KARANTA: Matsananciyar Yunwa Na Kashe Ƴan Nigeria, PDP Ta Faɗawa Buhari

Sojojin Kasar Isra'ila sun mayar da martani mai zafi a kan wuraren da Hamas suke a yankin na Gaza.

Shugabannin kasashe da kungiyoyi sun yi ta kiraye-kiraye ga bangarorin biyu su tsagaita wuta domin warware matsalar ta hanyar diflomasiyya.

A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.

Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel