Ku Taimaka in Sauke Wannan Nauyin da Aka Ɗora Mun, Gwamna Masari

Ku Taimaka in Sauke Wannan Nauyin da Aka Ɗora Mun, Gwamna Masari

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya roƙi al'ummar jihar sa su taimaka masa ya sauke nauyin shugabancin da suƙa ɗora masa

- Masari yace tun sanda ya shiga ofis ɗin gwamna a watan Mayu 2015, ya fara shirye-shiryen fita

- Yace gwamnatinsa na iya bakin ƙoƙarinta wajen sauke haƙƙin dake kanta, sannan ya nemi taimakon mutane wajen dawo da zaman lafiya a jihar

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa ya fara shirye-shiryen barin ofis tun ranar da aka rantsar dashi a watan Mayu, 2015, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna

Masari, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin wakilan ma'aikatan jihar wanda babban alƙalin jihar, Justice Abubakar Musa Ɗanladi, ya jagoranta domin yi masa Barka da sallah a gidan gwamnati.

Masari yace gwamnatinsa tana gudanar da al'amuran mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadar kuma tana baiwa duka ɓangarorin gwamnati uku damar gudanar da ayyukansu.

Ku Taimaka in Sauke Wannan Nauyin da Aka Ɗora Mun, Gwamna Masari
Ku Taimaka in Sauke Wannan Nauyin da Aka Ɗora Mun, Gwamna Masari Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

Gwamnan yace: "Gwamnatin mu ta rungumi masu rike da mukaman siyasa da kuma ma'aikata daban-daban na jihar da zuciya ɗaya, domin amfanin al'ummar mu, bawai don mu burge wasu tsirarun mutane ba."

"Nayi iya bakin ƙoƙarina ganin na baiwa masu riƙe da manyan ofisoshi damar yin aiki ƙarƙashin doka, hakanan na bar kofa ta a buɗe garesu, domin dawo da aminci da yarda da juna."

"Tun daga lokacin da na shiga ofishin gwamnan jihar nan, na fara shiryawa zuwan ranar da zan fita, ina fatan zan sauka cikin aminci idan lokacina ya ƙare."

KARANTA ANAN: Kamfanin Wutar Lantarki Ya Katse Duka Layukan Wutar Jihar Kaduna

Gwamnan yayi kira ga jama'ar jihar da su taimaka wa gwamnatinsa a ƙoƙarin da take na magance matsalar tsaro, farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma ƙalubalen ɓangaren lafiya.

Shugaban wakilan ma'aikatan gwamnati, Justice Abubakar, yace sun zo ne suyi wa gwamnan barka da Sallah da kuma fatan akairi.

Yace zasu cigaba da baiwa gwamnan goyon baya domin kawo cigaba a faɗin jihar.

"Ina kira ga masu riƙe da manyan ofisoshi da kuma ma'aikakata da su aje banbancin siyasa a gefe ɗaya,su bayar da gudummuwar su wajen kawo cigaba a jihar." inji shi.

A wani labarin kuma Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

Musulmi 29 ne aka yanke wa hukuncin kisa a jamhuriyar demokaraɗiyyar Kongo saboda rikici a filin sallar Idi.

A yayin rikin tsakanin ƙungiyoyin musulmi biyu, jami'in ɗan sanda ɗaya ya rasa rayuwarsa tare da jikkata wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel