'Yan bindiga sun kaiwa basarake a arewa farmaki har cikin fadarsa, sun yi muguwar barna

'Yan bindiga sun kaiwa basarake a arewa farmaki har cikin fadarsa, sun yi muguwar barna

- Miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki har cikin fadar basarake a jihar Binuwai

- Sun tsinkayi fadar ne wurin karfe 1:45 na daren ranar Juma'a inda suka lalata dukiyar miliyoyin naira

- Kamar yadda kanin basaraken ya sanar, ba a tarar da basaraken ba, lamarin da yasa 'yan bindigan suka yi fashe-fashe

'Yan bindiga sun kai farmaki fadar Kindred na Jor Fada, Terhile Atser dake Gboko.

Sun lalata kadarorin miliyoyin naira yayin da suka kai harin a cikin ranakun karshen mako.

Fadar shugaba Kindred tana nan a lamba 36 titin Kyado, Gboko ta gabas, karamar hukumar Gboko ta jihar Binuwai.

Kadarorin da suka salwanta yayin harin sun hada da motoci, babura da sauransu.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi

'Yan bindiga sun kaiwa basarake a arewa farmaki har cikin fadarsa, sun yi muguwar barna
'Yan bindiga sun kaiwa basarake a arewa farmaki har cikin fadarsa, sun yi muguwar barna. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Har yanzu dai ba a san dalilin kai harin ba kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kanin basaraken mai suna Robert Nomishu, ya sanar da manema labarai cewa maharan da suka kai biyar sun tsinkayi fadar wurin karfe 1:45 na daren Juma'a.

Sun rufe fuskokinsu da takunkumin fuska kuma suna dauke da bindigogi, adduna da sauran makamai kuma sun bukaci ganin sarkin amma sai aka ce musu baya nan.

Yace sun karasa ciki inda suka fasa tagogi da kofofi wanda suka kwashe sa'a daya suna yi tare da duba basaraken amma basu gan shi ba.

Ba a rasa rai ba yayin harin amma an mika rahoto ga ofishin 'yan sanda na Gboko dake yankin.

Har a halin yanzu rundunar 'yan sandan jihar Binuwai dake garin Makurdi basu yi martani a kan lamarin ba.

KU KARANTA: Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa

A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce "dukkan 'yan Najeriya" ne suke bukatarsa da ya nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A yayin jawabi a ranar Juma'a yayin da ake yin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai bada ansa ga wannan bukatar nan babu dadewa.

Gwamnan yace 'yan Najeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel