Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano

Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano

- Dan sanda mai suna Sajan Kabiru Isah dake aiki a Kano ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari

- An gano cewa wanda hatsarin ya ritsa dashi ya rasu bayan babbar mota ta bi ta kansa yayin da yake kan babur

- A matsayin jinjina da yabawa, shugaban KAROTA ya baiwa jami'in dan sandan kyautar N100,000

Jami'in dan sanda a Kano mai suna Sajan Kabiru Isah dake aiki da ofishin 'yan sanda na MTD ya mayar da N1,294,200 da ya tsinta a wurin wani hatsari da aka yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, jami'in dan sandan ya tsinta kudin ne yayin da yaje duba yanayin hatsari mintoci kadan bayan hatsarin.

Babbar mota ce a kan babban titin Zaria ta bige wanda hatsarin ya hada da shi a garin Kano yayin da yake kan babur din sa kuma yake dauke da makuden kudaden.

KU KARANTA: Da duminsa: JAMB ta bada sabuwar muhimmiyar sanarwa kan jarabawar UTME ta 2021

Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano
Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kada ku yi kasa guiwa wurin neman taimako daga Najeriya, Buhari ga Shugaban Chadi

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko, yayin mika kudin ga 'yan uwan mamacin, yayi kira ga jami'an 'yan sandan tare da mutanen jihar da su yi koyi da irin halin da jami'in ya nuna.

Ya kara da jinjinawa jami'in a kan aikinsa da yayi kamar yadda sifeta jana na 'yan sandan Najeriya, IGP Alkali Baba Usman ya umarta.

Amma kuma, cike da jin dadin halin da dan sandan ya nuna, manajan daraktan hukumar KAROTA, Dr Baffa Babba Dan Agundi, ya baiwa jami'in kyautar N100,000.

A yayin mika kudin, KAROTA ta ce tana matukar farin ciki da samun jami'in nan a yankin kuma tayi kira ga jama'ar jihar da su yi koyi da kyakyawan halin da jami'in ya nuna.

Baffa yace, "Muna godiya ga 'yan sanda a kan abinda suke yi a Kano kuma dole ne mu basu goyon bayan da ya dace da hadin kai."

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, yace tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, janar Joshua Nimyel Dogonyaro, kafin rasuwar shi ya bashi shawara kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar.

Ya kara da cewa marigayin janar din yayi babban kokari wurin baiwa kasar Najeriya kariya, Daily Trust ta ruwaito.

Lalong, wanda ya ziyarci iyalin marigayin domin ta'aziyya a Rayfield Jos, ya ce marigayi Dogonyaro ya nuna hazakarsa ta yadda ya bautawa kasar nan a yayin da yake aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: