Dubban Mutane Sun Yi Zanga-Zanga a Birnin Landan Kan Muzgunawa Falasdinawa
- Dubban mutane sun taru a birnin Landan don nuna kiyayyarsu ga kisan Falasdinawa a Gaza
- An ruwaito cewa, sama da mutane 150,000 suka taru a bakin ofishin jakadancin kasar Isra'ila
- Rikicin na Gaza ya lakume mutane da dama, ciki har da kananan yara sakamakon harbe-harbe
Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun yi jerin gwano zuwa ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Landan don kira ga daukar matakin gaggawa daga gwamnati don kawo karshen mummunan muzgunawa da ake yi wa Falasdinawa a rikicin Gaza.
Rikicin na Gaza ya tilasta wa dubban Falasdinawa barin gidajensu saboda yawan asarar rayuka da dukiyoyi.
Jaridar Punch a baya ta ba da rahoton cewa Shugaba Recep Erdogan na Turkiyya ya yi kira ga Shugaban, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da ya ba da hadin kai ga Falasdinawa bayan sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai wa Kudus da Gaza.
KU KARANTA: Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge ’Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano
Cikin hadin kai, dubban mutane sun fito kan titunan Landan don rera taken "'Yanta Falasdinu" don nuna adawa da rikicin Gaza.
Masu zanga-zangar sun hadu a Hyde Park kusa da Marble Arch don fara jerin gwanon a tsakar ranar Asabar.
A cewar DailyMail, ana ganin masu zanga-zangar suna toshe gine-gine, suna hawa kofofi, tare da hawa saman fitilun kan hanya a bakin ofishin jakadancin Isra’ila da ke Kensington a Landan.
Wadanda suka shirya zanga-zangar sun bayyana cewa an kiyasta masu zanga-zangar cewa sun haura mutum 150,000 a adadi, wanda hakan ya zama zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinu mafi girma tun 2014.
Rikicin na Gaza ya lakume rayukan mutane kusan 126, ciki har da kanan yara 31 da mata 20 sakamakon luguden wuta, da kuma daruruwan roka da aka harba tsakanin Isreala da Falasdinawa.
KU KARANTA: Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12 a Delta
A wani labarin, Jaridar The Cable ta ce shugaban kasar Turkiyya ya kira Mai girma Muhammadu Buhari, ya na neman Najeriya ta taimaka wa kasar Falastina da goyon baya.
Majiyar ta ce Recep Erdogan ya fada wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari cewa ya na sa ran kasarsa ta nuna goyon bayanta ga mutanen kasar Falasdina.
Recep Erdogan ya yi wannan kira ne bayan hare-haren da kasar Israila ta kai wa Jerusalem da Gaza a lokacin da ya zanta da shugaban Najeriya a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng