Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi

Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi

- Gwamna Lalong na jihar Filato ya ce marigayin janar Dogonyaro ya bashi shawarwari kan shawo kan matsalar tsaro

- Kamar yadda gwamnan ya bayyana yayin da yaje ta'aziyyar marigayin, yace a shirye yake kafin rasuwarsa domin bada gudumawa kan tsaro

- Gwamnan yayi addu'ar samun rahamar Ubangiji ga marigayin tare da juriya ga iyalansa na wannan babban rashin

Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, yace tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, janar Joshua Nimyel Dogonyaro, kafin rasuwar shi ya bashi shawara kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar.

Ya kara da cewa marigayin janar din yayi babban kokari wurin baiwa kasar Najeriya kariya, Daily Trust ta ruwaito.

Lalong, wanda ya ziyarci iyalin marigayin domin ta'aziyya a Rayfield Jos, ya ce marigayi Dogonyaro ya nuna hazakarsa ta yadda ya bautawa kasar nan a yayin da yake aikinsa.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni

Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi
Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci

Ya ce marigayin yana yawan shawartarsa a kan yadda zai shawo kan matsalar tsaro kuma ya shirya tsaf domin bada gudumawa da gogewarsa wurin hada kan jama'a daban-daban.

Yayi addu'a Ubangiji ya baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa kuma yayi kira garesu da su cigaba a kan turbar da marigayin ya bar su.

A yayin martani a madadin iyalan, Godfrey Dungum, ya ce ziyarar gwamnan da mukarrabansa ta matukar kwantar musu da hankali.

Ya nuna godiyarsa akan goyon baya da karamcin da gwamnatin lalong take cigaba da baiwa janar din a rayuwarsa da bayan mutuwarsa.

A wani labari na daban, daya daga cikin shugabannin miyagun 'yan bindigan da suka dade suna addabar jihar Neja, ya shiga hannun dakarun rundunar sojin Najeriya.

Shugaban 'yan bindigan wanda ake kira da Jack Bros Yellow ya shiga hannu ne sakamakon ayyukan da sojojin suke yi a fadin dajikan jihar Neja.

Rahotannin tsaron da jaridar The Nation ta samu sun bayyana cewa an kama Yellow ne a daya daga cikin dajikan dake tsakanin karamar hukumar Rafi da Shiroro.

Rundunar sojin Najeriya ta yi shiru a kan ayyukan da take a dajikan saboda yadda wasu ke kaiwa 'yan bindigan bayanai domin zagon kasa ga kokarin dakarun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel