Da duminsa: Sojin Najeriya sun cafke Jack Bros Yellow, shugaban 'yan bindigan Neja

Da duminsa: Sojin Najeriya sun cafke Jack Bros Yellow, shugaban 'yan bindigan Neja

- Jack Bros Yellow, daya daga cikin gagaruman shu'uman shugabannin 'yan bindigan jihar Neja ya shiga hannun hukuma

- An gano cewa dan ta'addan yana da alaka da wasu kungiyoyin 'yan bindigan da suke jihar Zamfara

- Mazauna yankin sun ce shine shugaban 'yan bindigan da suka addabi kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya

Daya daga cikin shugabannin miyagun 'yan bindigan da suka dade suna addabar jihar Neja, ya shiga hannun dakarun rundunar sojin Najeriya.

Shugaban 'yan bindigan wanda ake kira da Jack Bros Yellow ya shiga hannu ne sakamakon ayyukan da sojojin suke yi a fadin dajikan jihar Neja.

Rahotannin tsaron da jaridar The Nation ta samu sun bayyana cewa an kama Yellow ne a daya daga cikin dajikan dake tsakanin karamar hukumar Rafi da Shiroro.

KU KARANTA: Farmaki a Aso Rock: An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa

Da duminsa: Sojin Najeriya sun cafke Jack Bros Yellow, shugaban 'yan bindigan Neja
Da duminsa: Sojin Najeriya sun cafke Jack Bros Yellow, shugaban 'yan bindigan Neja. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

KU KARANTA: Gurfanar da Diezani: EFCC ta jero manyan kalubalen da take fuskanta

Rundunar sojin Najeriya ta yi shiru a kan ayyukan da take a dajikan saboda yadda wasu ke kaiwa 'yan bindigan bayanai domin zagon kasa ga kokarin dakarun.

Har a halin yanzu rundunar sojin bata tabbatar da kamen ba amma majiya daga yankin ta bayyana cewa Jack Bros Yellow shine shugaban daya daga cikin miyagun kugiyoyi uku na 'yan bindiga da suka dade suna addabar kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya.

Majiyar ta kara da Bayyana cewa akwai yuwuwar shugaban 'yan bindigan yana da alaka da wasu miyagun kungiyoyin 'yan bindigan dake Zamfara.

An gano cewa, sau da yawa yana mika wadanda ya sata amma basu biya kudi da wuri ba zuwa wasu kungiyoyin 'yan bindigan dake Zamfara.

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel