Kada ku yi kasa guiwa wurin neman taimako daga Najeriya, Buhari ga Shugaban Chadi
- Shugaban kasa Buhari ya bukaci kasar Chadi da kada tayi kasa a guiwa wurin neman taimako daga Najeriya
- Buhari ya kara da jaddada cewa Najeriya za ta taimakwa jamhuriya Chadi wurin komawa mulkin damokaradiyya
- Buhari ya ce marigayi Deby abokinsa kuma abokin kasar nan ne domin ya taka rawa wurin yakar ta'addanci
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugaban kasan rikon kwarya na soji na kasar Chadi, Laftanal Janar Mahamat Idris Deby Itno da kada su yi kasa a guiwa wurin neman taimako daga Najeriya a duk lokacin da suke bukatar hakan.
Shugaban kasan ya kara da daukan alkawarin cewa zai taimaki jamhuriyar Chadi wurin samun daidaito da kuma komawa kundun tsarin Mulki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin Janar Deby Itno a fadarsa dake Aso Villa, Abuja.
KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin sallar idi, cikin 'yan majalisa da iyalansa a Aso Rock
KU KARANTA: Da duminsa: Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya ya rasu
Idan zamu tuna, Marshal Idris Deby Itno, tsohon shugaban kasan Chadi ya rasu yayin da ya jagoranci sojin kasar wurin yaki da 'yan ta'adda wadanda suka shiga kasar ta Libya.
Kasar ta kafa gwamnatin rikon kwarya wanda ke samun shugabancin dan mamacin kuma ana tsammani zasu koma mulkin damokaradiyya bayan watanni 18.
Kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar a wata takardar da mai bada shawara ta musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce "Mun hadu ne a bangaren kasa da kuma al'ada kuma zamu yi duk yadda ya dace wurin ganin mun taimaka."
Ya kara da sanar da bakonsa cewa, "Yan Najeriya sun sani kuma sun gode da irin rawar da Chadi ta taka wurin yakar ta'addanci kuma zamu cigaba da bada hadin kai."
Shugaban kasan yace marigayi Marshal Itno "abokina ne kuma abokin Najeriya. Chadi ta kasance kan gaba wurin baiwa Najeriya kariya," don haka kada kasar tayi kasa a guiwa wurin neman taimako idan akwai bukatar hakan.
"Zamu kara da taimaka muku wurin komawa mulkin damokaradiyya hankali kwance a cikin watanni 18 din da kuka yi wa jama'arku alkawari."
A wani labari na daban, Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.
Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.
Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan."
Asali: Legit.ng