Da duminsa: JAMB ta bada sabuwar muhimmiyar sanarwa kan jarabawar UTME ta 2021

Da duminsa: JAMB ta bada sabuwar muhimmiyar sanarwa kan jarabawar UTME ta 2021

- Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta ce akwai yuwuwar ta sauya lokacin rubuta UTME ta 2021

- Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya sanar da hakan a yayin ganawar da yayi da masu ruwa da tsaki a ranar Juma'a

- Farfesan yace wannan cigaban zai zo ne sakamakon yadda dalibai suke shan wahala yayin yin rijistar jarabawar

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta fara magana a kan yuwuwar sauya lokacin rubuta jarabawar na shekarar 2021.

Dama za a rubuta jarabawar ne daga ranar 6 ga watan Yunin 2021 zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2021.

Hukumar shirya jarabawar amma ta tabbatar da cewa za a rubuta jarabawar gwajinta a ranar 20 ga watan Mayun 2021 bayan sauya ranar da tayi.

Hukumar ta ce hukuncin dage jarbawar ko rubutata za a yanke shi ne a ranar Juma'a bayan kammala taro tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA: Gurfanar da Diezani: EFCC ta jero manyan kalubalen da take fuskanta

Da duminsa: JAMB ta bada sabuwar muhimmiyar sanarwa kan jarabawar UTME ta 2021
Da duminsa: JAMB ta bada sabuwar muhimmiyar sanarwa kan jarabawar UTME ta 2021. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin sallar idi, cikin 'yan majalisa da iyalansa a Aso Rock

Rijistra na hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya sanar da hakan a ranar Juma'a yayin taron da yayi da masu ruwa da tsaki a kan jarabawar ta yanar gizo.

Farfesa Oloyede ya dora laifin wannan cigaban a kan wahalar da dalibai masu rijistar jarabawar ke samu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya ce a kalla dalibai 600,000 ne suka bayyana ra'ayinsu na rubuta jarabwar UTME ta 2021 amma har yanzu sun kasa yin rijista.

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel