Gurfanar da Diezani: EFCC ta jero manyan kalubalen da take fuskanta

Gurfanar da Diezani: EFCC ta jero manyan kalubalen da take fuskanta

- Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa suna fuskantar manyan kalubale a kokarinsu na gurfanar da Diezani

- Shugaban ya bayyana cewa zamanta a Birtaniya tun daga 2015 ya kasance babban kalubale garesu a yayin kokarin dawo da ita gida

- Ya sanar da yadda suka samo kudi har $153 miliyan tare da gidaje 80 masu darajar $80 miliyan a Najeriya

Shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulerasheed Bawa, yace dawo da tsohuwar ministan fetur, Diezani Alison Maduke gida tare da gurfanar da ita ba wasa bane.

Ya ce saboda tsohuwar ministar bata karkashin ikon Najeriya a yanzu tare da kalubalen da za a iya fuskanta wurin dawo da ita har yau sune manyan kalubale.

Wannan na kunshe a wata mujallar EFCC mai suna EFCC Alert wacce aka fitar a watan Afirilu, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa hukumar ta samo $153 miliyan daga tsohuwar ministan wacce ta koma zama a Birtaniya tun bayan da ta sauka daga kujerarta a 2015.

KU KARANTA: Da duminsa: Rundunar 'yan sanda a Binuwai ta gano wasu kaburburan sirri

Gurfanar da Diezani: EFCC ta jero manyan matsalolin da take fuskanta
Gurfanar da Diezani: EFCC ta jero manyan matsalolin da take fuskanta. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo a bude, sun bukaci Buhari yayi wa kasa jawabi

Bawa ya kara da cewa hukumar ta kwace a kalla gidajen alfarma 80 wadanda darajarsu za ta kai $80 miliyan daga wurin tsohuwar ministan.

Shugaban yace, "Akwai abubuwa da yawa dake zagaye da lamarin Diezani. Ina cikin masu binciken kuma mun yi nisa, A daya daga cikin bincikenmu, mun samo $153 miliyan, mun kwace gidajenta 80 a Najeriya masu darajar $80 miliyan. Mun yi nisa gaskiya a kan hakan.

"Akwai wani bincike na $115 miliyan da ya danganci cin hancin hukumar zabe a fadin kasar nan. Muna fatan lokaci da zai zo inda zata kasance a kasar nan kuma mu cigaba. Babu shakka ba zamu bar ta ba."

A wani labari na daban, a kalla mutum hudu aka kama wadanda ake zargi da alaka da 'yan bindigan daji, satar shanu, garkuwa da mutane tare da fashi da makami a jihar Katsina, Channels TV ta ruwaito.

Wadanda ake zargin, kamar yadda hukumar 'yan sandan jihar ta sanar, 'yan wata gagarumar kungiyar 'yan ta'adda ce da suka addabi karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina da kewaye.

A wani jawabi ga manema labarai a ranar Talata, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah yace sun kama wadanda ake zargin ne bayan bayanan sirri da suka samu a ranar 10 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel