Farmaki a Aso Rock: An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa

Farmaki a Aso Rock: An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa

- Farmakin da wasu barayi suka kai fadar shugaban kasan Najeriya ya tada hankulan jama'a

- Bincike ya nuna cewa gidan da ba rayin suka yi yunkurin shiga ya kasance madaddalar 'yan kwangila

- A tunanin barayin, ana ajiye makuden kudade a gidan saboda yadda 'yan kwangila ke kaiwa da kawowa

A kalla 'yan sanda hudu ne ke tsaron gidan Maikano Abdullahi, jami'in fadar shugaban kasa wanda wasu barayi suka yi yunkurin shiga gidansa.

An gano cewa jami'an tsaro biyu ke aiki a lokaci daya, rana biyu, dare biyu a gidan, jaridar The Punch ta ruwaito.

Gidan yana da kusanci da gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke da kusancin mitoci kadan da wani wurin da sojoji hudu ke zama.

KU KARANTA: Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

Farmaki a Aso Rock: An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa
Farmaki a Aso Rock: An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Rundunar 'yan sanda a Binuwai ta gano wasu kaburburan sirri

Duba da aka yi an gano cewa gidan yana cikin fadar shugaban kasa ne kuma ana matukar tsaronsa domin kuwa har da maharban boye akwai.

Gidan an gano ya kasance madaddalar 'yan kwangila da ke neman kafa ta wurin Abdullahi domin samun shiga a fadar shugaban kasan akan lamurran kwangilolinsu.

Majiya daga jami'an tsaro ta ce ta yuwu barayin sun yi tsammanin ana ajiye makuden kudade a gidan ne yasa suka kai farmakin.

An gano cewa dan sanda dauke da bindiga ne ya fatattaki barayin yayin da yake kan aikinsa.

Barayin da suka tsallaka katanga ta wani layin baya sun arce bayan ganin dan sandan dake farfajiyar domin tseratar da rayukansu.

Wata majiya tace, "Abinda ya faru shine barayi sun fado ta katanga daga titin baya amma sai suka tarar da dan sanda. Hakan yasa sun sake tsallaka katangar tare da tserewa."

A wani labari na daban, a kalla mutum hudu aka kama wadanda ake zargi da alaka da 'yan bindigan daji, satar shanu, garkuwa da mutane tare da fashi da makami a jihar Katsina, Channels TV ta ruwaito.

Wadanda ake zargin, kamar yadda hukumar 'yan sandan jihar ta sanar, 'yan wata gagarumar kungiyar 'yan ta'adda ce da suka addabi karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina da kewaye.

A wani jawabi ga manema labarai a ranar Talata, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah yace sun kama wadanda ake zargin ne bayan bayanan sirri da suka samu a ranar 10 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel