Hoton Hadiza Bala Usman Da El-Rufai a Fadar Sarkin Zazzau Ya Janyo Maganganu

Hoton Hadiza Bala Usman Da El-Rufai a Fadar Sarkin Zazzau Ya Janyo Maganganu

- Hadiza Bala Usman, Shugaban NPA da aka dakatar ta yi wa Gwamna Nasir El-Rufai rakiya zuwa fadar sarkin Zazzau

- Hadiza ta wallafa hoton da ta dauka tare da El-Rufai inda ta bayyana shi a matsayin 'mai gidanta na har abada'

- Har wa yau, Hadiza ta yi magana a kaikaice game da binciken da ake mata na zargin karkatar da kudi Naira biliyan 165

- Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan maganar ta inda wasu ke ganin sharri ake son mata wasu kuma akasin haka

Shugaban hukumar kula da jiragen ruwa na kasa NPA da aka dakatar, Hadiza Bala Usman, a ranar Alhamis ta bayyana a bainar mutane karon farko a yayin da ake bincike a hukumar ta.

Bala Usman ta yi wa gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai rakiya ne zuwa fadan sarkin Zazzau, Mai Martaba Ambasada Ahmad Nuhu Bammali domin yi masa gaisuwar sallah karama.

'Har Gobe El-Rufai Mai Gida Na Ne', Hadiza Bala Usman Ta Magantu a Karon Farko
'Har Gobe El-Rufai Mai Gida Na Ne', Hadiza Bala Usman Ta Magantu a Karon Farko. @hadizabalausman
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsige Buhari Ba Zai Samar Da Tsaro a Nigeria Ba, Sanata Yusuf

A ranar Litinin, Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya kafa kwamitin bincike don duba dukkan kwangilolin da aka yi a NPA karkashin mulkinta.

An dakatar da Bala Usman ne a ranar Juma'a kan zargin rashin biyan Naira Biliyan 165 a asusun tara haraji na kasa (CFR).

Amma ta musanta wannan zargin.

A wani rubutu da ta wallafa a ranar Alhamis a Twitter, ta yi magana a kaikace gami da dakatarwarta tana mai cewa gaskiya za ta yi halinta.

Ta kuma jadada biyayyarta ga Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna wanda ta bayyana a matsayin 'Mai gidanta na har abada'.

Bala Usman ce shugaban ma'aikatan fadar El-Rufai a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta shugaban NPA a 2016.

"Eid Mubarak ... ”Taqabbalallāhu minnā wa minkum” Allah ya karbi ayyukanku da namu" A fadar Sarkin Zazzau tare da mai gida na na har abada @elrufai. Mun yi imani cewa gaskiya za ta yi halinta ... Allah ya kiyaye mu ya yi mana jagora a kowanne lokaci," kamar yadda ta rubuta.

Hoton da Hadiza ta wallafa da rubutun ya dauki hankalin mutane masu amfani da Twitter inda wasu suka rika goyon bayanta suna taya ta addu'a yayin da wasu kuma akasin haka.

@@PrinceNdAkpan ya ce, "Babu wani gaskiya da zai fito, wannan batu ce ta nuna isa, wasu masu iko suna ganin ba ki 'girmamasu' yadda suke so, za su nuna miki cewa sun dade a harkar kafin ki shigo."

Sun san ba kiyi laifi ba, kawai suna son yin waje da ke ne. Haka siyasa ta ke."

@EjioforOnyishi ya ce, "Amaechi da mukarabbansa za su 'ragargaje ku' sai dai idan kun yi abin da suke so."

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel