Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga

Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga

- Alhaji Abbas Njidda Tafida, sarkin Muri a jihar Taraba ya umurci mutane su dena jin tsoron yan bindiga

- Sarkin ya bukaci mutanen masarautarsa su rika yin fito-na-fito da yan bindiga a maimakon tserewa idan sun kawo hari

- Sarkin ya ce yan bindigan ba su da yawa idan aka kwatanta su da yawan mutanen gari don haka a dena kyalle su suna cin karensu babu babbaka

Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida ya umurci mutanen masarautarsa su yi fito-na-fito da masu garkuwa da mutane da yan bindiga a maimakon su rika tserewa idan sun kawo musu hari, Daily Trust ta ruwaito.

Sarkin ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu a lokacin da mutane suka kai masa gaisuwar sallah yana mai cewa bata garin da ke adabar mutane kalilan ne idan aka kwatanta su da mutanen gari.

DUBA WANNAN: Hoton Hadiza Bala Usman Da El-Rufai a Fadar Sarkin Zazzau Ya Janyo Maganganu

Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga
Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ya kallubalanci mutanensa su zama jarumai su kuma kare garuruwansu.

"Idan sun kashe wani a unguwanku, su mayar da martani ku kashe su ba tserewa za ku yi ba ku kyallesu su kashe ku ko kuma su sace mutanenku," in ji shi.

"Ya kamata jama'an gari su dena yarda da harin da masu garkuwa ke kai musu ta hanyar yin fito-na-fito da su duk lokacin da suka kawo hari."

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kai Samame Maɓuyar IPOB Sun Kama Babban Kwamanda

Sarkin ya kuma bada shawarar cewa a gina ganuwa a iyakokin kauyuka da birane saboda kariya kamar yadda ake yi a zamanin iyaye da kakanni.

Ya umurci mutane su rika zama cikin shiri su kuma sa ido a garuwansu.

A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.

Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel