Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kai Samame Maɓuyar IPOB Sun Kama Babban Kwamanda

Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kai Samame Maɓuyar IPOB Sun Kama Babban Kwamanda

- Hukumar soji ta sanar da cafke mataimakin babban kwamandan ESN Awurum Eze

- Wata tawagar jami'an da suka hada da sojoji, yan sanda, da jami'an farin kaya ne suka yiwa hedikwatar ESN kawanya

- Mr Eze na da alaka ta kusa da Nnmadi Kanu, jagoran fafutukar kafa kasar Biafra

Rundunar sojin Najeriya ta kama Awurum Eze, babban mataimakin kwamandan Eastern Security Network ESN, wata rundunar jami'an tsaron haramtacciyar Biafra, IPOB.

Mai magana da yawun rundunar soji, Mohammed Yerima, shine ya bayyana haka ranar Laraba.

A cewar sa, Mr Eze shine mataimakin Ikonso, kwamandan ESN wanda aka kashe a musayar wuta da jami'an tsaro kwanakin da suka gabata.

Da Duminsa: Sojoji Sun Kai Samame Mabuyar IPOB Sun Kama Mataimakin Ikonso
Da Duminsa: Sojoji Sun Kai Samame Mabuyar IPOB Sun Kama Mataimakin Ikonso. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram 8 Cikin Waɗanda Suka Kai Hari Maiduguri Sun Baƙunci Lahira

Premium Times ta ruwaito yadda wata tawagar jami'an tsaro da ta hada da jami'an soji, yan sanda, da kuma jami'an farin kaya (SSS) sun mamaye hedikwatar ESN din.

A kalla mutane 11 suka mutu a musayar wutar da suka hadar da jami'an tsaro hudu da kuma wani mutum da aka bayyana a matsayin babban mataimakin kwamandan ESN, a cewar wani jami'i.

A cewar hukuma, an kashe Mr Ikonso a wata musayar wuta da jami'an tsaro tare da wasu kwamandojin sa guda shida.

Hukumomin tsaro sun zargi kungiyar, wanda ke son a basu kasar Igbo mai cin gashin kanta, da hannu wajen kaiwa jami'an tsaro da wasu muhimman wurare hari amma IPOB sun karyata zargin kai hare haren.

An kashe jami'an tsaro da dama a haren haren da ake kaiwa kudu maso yamma da kudu maso gabas kan jami'an tsaro da muhimman wurare.

KU KARANTA: Wani Mutum Ya Kashe Ɗan Sanda a Zamfara Bayan Cacar-Baki Kan Cin Abinci Yayin Azumin Ramadan

A wata sanarwa ranar Laraba, sojoji sun ce Mr Eze na daya cikin manyan masu daukar nauyin haren haren da ake kaiwa jami'an tsaro a Jihar Imo.

Sanarwar ta kuma ce Mr Eze da Ikonso suna da alaka ta kai tsaye da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel