Wani Mutum Ya Kashe Ɗan Sanda a Zamfara Bayan Cacar-Baki Kan Cin Abinci Yayin Azumin Ramadan
- Dan sanda a jihar Zamfara ya mutu sakamakon fada da wani farar hula mai suna Alage Mukhtari
- Dan sandan ya siya burodi da lemun kwalba yana sha ne da rana tsaka ana azumi shi kuma Mukhtar ya rika masa kallon 'banza'
- Dalilin kallon da dan sandan bai gamsu da shi ba sai ya cire damara ya fara dukar farar Mukhtari, garin kare kansa ya halaka dan sandan
Wani jami'in dan sanda ya rasa ransa wurin fada da farar hula saboda cin abinci a lokacin azumin watan Ramadan, The Punch ta ruwaito.
Wani mazaunin yankin, Abdullahi Damba ya ce dan sandan na cin burodi ne yayin azumin Ramadan sai wani Alage Mukhtari ya rika masa kallo mara dadi.
DUBA WANNAN: Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun
Abdullahi ya ce, "Dan sandan ya siya burodi da lemun kwalba ya fara ci sai Muktari, wanda ke cikin shagon ya fara masa wani irin kallo."
"Irin kallon da Muktari ke yi wa dan sandan yasa ya fusata ya tambaye shi dalilin da yasa ya ke masa irin wannan kalon."
"A cewar Abdullahi, dan sandan ya cire damararsa ya fara dukan Muktari shi kuma a kokarin ya kare kansa, Muktari ya yi wa dan sandan mugun bugu wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ce, "An kama wanda ake zargi da kisar kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu."
A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.
Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.
Asali: Legit.ng