Babban Limamin Ibadan Ya Bijire Wa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idi

Babban Limamin Ibadan Ya Bijire Wa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idi

- Sheikh AbdulGaniy Agbotomokekere, babban limamin Ibadanland, ya jagoranci wasu Musulmai yin sallar Idi a Ibadan

- Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar, ya sanar a ranar Talata, 11 ga watan Mayu, cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Najeriya

- Abubakar ya bukaci Musulmi da su tashi da azumin Ramadana a ranar Laraba, 12 ga watan Mayu

Babban Limamin Ibadanland, Sheikh AbdulGaniy Abubakar Agbotomokekere, a ranar Laraba, 12 ga Mayu, ya bijire wa umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar na yin azumi saboda rashin bayyanar sabon jinjirin watan Shawwal.

Wakilin Legit.ng a yankin Ibadan, Ridawan Kolawole, ya ruwaito Sheikh Agbotomokekere ya jagoranci wasu yan tsirarun musulmai don yin sallah a yankin Agodi da ke tsohon garin.

Mai kula da harkokin yada labarai na Limamin, Ustadh Idris Agbotomokekere, ya ce umarnin Babban Limamin na kan ganin sabon jinjirin wata.

Babban Limamin Ibadan Ya Bijire Wa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idi
Babban Limamin Ibadan Ya Bijire Wa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idi Hoto: Ridwan Kolawole/@NSCIAng
Asali: Original

KU KARANTA KUMA: Ku Ci Gaba Da Yiwa Najeriya Addu'a Har Bayan Ramadan – Saraki Ga Musulmai

Amma, malamin ya yi abin da ya saba wa maganar Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya karkashin jagorancin shugabanta-Janar kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar.

Sultan din a ranar Talata 11 ga Mayu, ya sanar da Musulman Najeriya cewa saboda rashin bayyanar jinjirin wata da ke nuna farkon watan Shawal, Ramadan zai kare a ranar Laraba, 12 ga Mayu.

Don haka, aka shirya gudanar da sallar Idi a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu, a cewar wani bayani daga Sarkin Musulmi.

Umarnin na Sultan ya yi daidai da fikihun Musulunci na kidayar Ramadan zuwa 30 idan ba a ga Shawwal ba.

Sai dai, Sheikh Agbotomokekere ya jagoranci wasu musulmai muminai don yin Idi wanda ya kawo karshen azumin Ramadhan.

Daga cikin manyan da suka halarci idin tare da Limamin sun hada da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Injiniya Rauf Olaniyan, shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar, Cif Taofeek Arapaja da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi

Da yake magana da Legit.ng, mai kula da shafukan sada zumunta na Babban Limamin na Ibadanland, Ustadh Idris Agbotomokekere, ya ce shawarar da Babban Limamin ya yi na bikin Idi ya biyo bayan matsayinsa na shugaban kungiyar limamai da malamai a Ibadanland.

A gefe guda, shahararren malamin nan na addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gabatar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba, 12 ga watan Mayu.

An tattaro cewa Shehin Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke garin Bauchi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa daya daga cikin 'ya'yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mabiya sallan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel