Ku Ci Gaba Da Yiwa Najeriya Addu'a Har Bayan Ramadan – Saraki Ga Musulmai

Ku Ci Gaba Da Yiwa Najeriya Addu'a Har Bayan Ramadan – Saraki Ga Musulmai

- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya taya daukacin al'umman Musulmi murnar kammala azumin Ramadana

- Saraki ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da yiwa kasar addu'a kan halin da take ciki har bayan Ramadan

- Ya kuma yi kira ga hadin kai, bin doka da kishin kasa a kowane lokaci

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki ya taya musulmai a Najeriya da ma duniya baki daya murnar kammala azumin watan Ramadan na wannan shekarar da bikin idi-El-Fitri.

Saraki a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Yusuph Olaniyonu, mai ba shi shawara na musamman a kafofin watsa labarai, ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kusantar Allah Madaukakin Sarki da kuma addu’o’in su na neman Ya shiga cikin lamuran kasar, ko da bayan azumin farilla.

Ya bayyana cewa azumin Ramadana ba kawai yana nuna halaye ne masu kyau ba amma yana wakiltar canji ne gaba daya wajen zama 'yan kasa na gari wadanda ke bin doka da nuna kishin kasa a kowane lokaci, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ku Ci Gaba Da Yiwa Najeriya Addu'a Har Bayan Ramadan – Saraki Ga Musulmai
Ku Ci Gaba Da Yiwa Najeriya Addu'a Har Bayan Ramadan – Saraki Ga Musulmai Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi

“Ya kamata mu guji komawa ga dabi’unmu na baya mu zama ‘yan kasa na gari masu yi wa kasa addu’a a kowane lokaci sannan mu taka rawar mu a kokarinmu na neman tsoron Allah, horo, hadin kai, ci gaba, daidaito, adalci da kuma hada kai a cikin harkokin siyasa .

“Halin da muke ciki yanzu a kasarmu yana bukatar canjin gaskiya daga dukkan ‘yan Najeriya. Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin bayan Ramadan da kuma darussan da muka koya daga lokacin yin azumi don kauce wa duk wani aiki da ba shi da kyau ga kasarmu. Wannan wani lokaci ne da ya kamata dukkanmu mu yi addu’a ga Allah Ya fitar da ƙasar daga ƙangi.

“Da matakin rashin tsaro da rikicin tattalin arziki wadanda suka hadu suka kara tabarbarewar talauci a Najeriya, ya zama dole duk ‘yan Najeriya su hada kai su nuna kishin kasa wanda zai taimaki kasarmu wajen shawo kan matsalolin da muke fuskanta.

“Har ila yau, ina yaba wa hukumomin tsaronmu da ke bakin daga ina addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya kiyaye ya kuma ba su nasara a kan masu tayar da kayar baya da sauran wadanda ke haddasa tashin hankali a kasarmu. Allah Ya warkar da kasarmu daga kowace irin masifa”, Saraki ya kara da cewa.

KU KARANTA KUMA: Karamar Sallah: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gudanar da Sallar Idi a Bauchi

A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 12 ga watan Mayu, ya roki ‘yan Najeriya da su yi addu’a a kan satar mutane, fashi da makami da batanci.

A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya yi kiran ne a sakonsa na Eid-il-Fitr wato bikin karamar Sallah.

An sanya wa sanarwar take da ‘A yayin bikin Idi, Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai’.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng