Karamar Sallah: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gudanar da Sallar Idi a Bauchi

Karamar Sallah: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gudanar da Sallar Idi a Bauchi

- Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gudanar da Sallar idi a gidansa da ke garin Bauchi a yau Laraba, 12 ga watan Maris

- Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, daya daga cikin 'ya'yansa shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mabiya sallan

- Shehin malamin ya ce sun yi Sallarsu ne saboda ba su da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin wata

Rahotanni sun kawo cewa shahararren malamin nan na addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gabatar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba, 12 ga watan Mayu.

An tattaro cewa Shehin Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke garin Bauchi.

KU KARANTA KUMA: Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi

Karamar Sallah: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gudanar da Sallar Idi a Bauchi
Karamar Sallah: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Gudanar da Sallar Idi a Bauchi Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa daya daga cikin 'ya'yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mabiya sallan.

Bayan kammala sallar, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce sun gudanar da sallarsu ta Idi ne saboda an tabbatar musu da ganin watan Shawwal a ranar Talata, 11 ga watan Mayu.

A cewarsa, "Dangane da wadannan labarai na cewa wata ya tabbata, abin da aka ce adilai guda biyu idan sun gani ya isar mana jama'a, ko kuma jama'a masu yawa (idan sun ga watan)."

Ya kara da cewa an ga wata a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi.

KU KARANTA KUMA: Wani Mutum Ya Kashe Ɗan Sanda a Zamfara Bayan Cacar-Baki Kan Cin Abinci Yayin Azumin Ramadan

A cewar shehin malamin, ba su da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin wata "saboda suna da yawa. Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da Sallar Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo."

A baya mun kawo cewa Kwamitin Sarkin Musulmi kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun sanar da cewa ba su samu labarin ganin watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadana.

Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar CFR, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel