Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi

Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi

- Sabon Khalifa na darikar Tijjaniya a Najeriya, Muhammad Sanusi II ya ce babu rashin jituwa a tsakaninsa da Sheikh Dahiru Bauchi

- Tsohon sarkin Kanon ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin uba a gare shi kuma mai goyon bayansa a koda yaushe

- Sanusi ya kuma sha alwashin kawo ci gaba ga kungiyar Tijjaniya da addinin Musulunci a kasar

Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa babu rashin jituwa a tsakaninsa da Sheikh Dahiru Bauchi.

Yayin da yake amsa tambaya kan ko Sheikh Dahiru Bauchi yana sane kuma ya yarda da tabbatar da shi a matsayin Khalifa, Malam Sanusi ya ce ba shi da wata matsala da Shehin malamin kuma shi kakansa ne, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan Sanda Sun Kama Manyan Masu Garkuwa da Mutane Su 6 a Abuja

Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi
Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi Hoto: Vanguard
Asali: UGC

“Sheikh Dahiru Bauchi bai taba fadin wani mummunan abu a kaina ba face soyayya da goyon baya. Shi mahaifina ne kuma babban amini ne ga kakana Sarki Muhammad Sanusi I.

“Abin da ya faru shi ne, Khalifa Sheikh Mahy Nyass ya tura ɗan’uwansa Sheikh Quraish zuwa Najeriya kuma ya zagaya ya nemi malamai da yawa da Muƙaddimai. Ya je kudancin Najeriya wani yanki kuma ya nemi ra'ayinsu kuma suka yarda.

"Duk da cewa su (Iyayen Nyass) sun kasance suna zaban wanda suke so ne kawai, amma babban Khalifa ya nemi a tuntubi malamai a Najeriya kuma sun zagaya dukkan sassan kasar kuma an ba da shawarar a nada ni," in ji shi.

Malam Sanusi ya ce yanzu zai fuskanci aikinsa a matsayinsa na Khalifa na Tijjaniyya don kawo ci gaba da hadin kai a tsakanin Musulmi.

“Nasara ta farko ita ce yadda kashi 98 na mutanenmu suka hada kai suka yanke shawarar zabar mutum daya a matsayin shugaba. Da zarar mutane sun aminta da shugabancin ka to akwai hadin kai. Yanzu zamu zo mu ga yadda zamu gano kalubalen da Tijjaniyya ke fuskanta da kuma yadda zamu magance su.

“Za mu kuma duba kalubalen da ke fuskantar dukkan Musulmi musamman a Arewacin Najeriya. Mabiya Tijjaniyya musulmai ne kuma yan asalin Najeriya. Akwai matsaloli a cikin ilimi, rikicin iyali, yara, Tsangaya da Zawiyyas; wadannan wasu batutuwa ne da za mu duba su sannan kuma mu fito da tsarin da zai nuna muna cikin karni na 21,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki

A baya mun ji cewa Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, babban Khalifa na darikar Tijjaniya, ya nada Sanusi Lamido Sanusi II a matsayin Khalifa na darikar Tijjaniya a Najeriya a ranar Lahadi a Senegal.

A watan Maris, an sanar da tsohon sarkin a matsayin Khalifan darikar Tijaniyya a taron shekara-shekara da ake yi a Sakkwato, TheCable ta ruwaito.

Bangarori biyu na darikar sun nada tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a matsayin Khalifansu a lokacin bikin Mauludin Inyass.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng