Bikin Karamar Sallah: Buhari Ya Bukaci Yan Najeriya da Su Yi Addu’a Kan Fashi Da Makami da Sace-Sacen Mutane

Bikin Karamar Sallah: Buhari Ya Bukaci Yan Najeriya da Su Yi Addu’a Kan Fashi Da Makami da Sace-Sacen Mutane

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon Sallah ga al'umman Musulmi yayinda suke kammala azumin Ramadana

- Buhari ya bukaci yan kasar dasu yi addu'an ganin karshen matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu

- Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da na addini da kuma sarakunan gargajiya da su karfafa hadin kai a kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 12 ga watan Mayu, ya roki ‘yan Najeriya da su yi addu’a a kan satar mutane, fashi da makami da batanci.

A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya yi kiran ne a sakonsa na Eid-il-Fitr wato bikin karamar Sallah.

An sanya wa sanarwar take da ‘A yayin bikin Idi, Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai’.

Bikin Karamar Sallah: Buhari Ya Bukaci Yan Najeriya da Su Yi Addu’a Kan Fashi Da Makami da Sace-Sacen Mutane
Bikin Karamar Sallah: Buhari Ya Bukaci Yan Najeriya da Su Yi Addu’a Kan Fashi Da Makami da Sace-Sacen Mutane Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Bukukuwan Sallah: Abubuwa 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Yi Kafin Sallar Idi

Shugaba Buhari ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kiyaye dukkan matakan rigakafin na COVID-19 da yin biki yadda ya kamata yayin hutun.

Shehu ya nakalto Shugaban kasar yana cewa, “A wannan biki mai albarka, ina fatan bikin Idi ya zo da zaman lafiya, aminci, tsaro, yan uwantaka da kauna a tsakanin duka mutane.

“Hadin kai a tsakanin dukkan ‘yan kasa, Musulmi da Kirista na da matukar muhimmanci musamman a lokacin da kasarmu ke fuskantar kalubale iri-iri wadanda ba za a iya shawo kansu ba sai idan mun hadu a matsayi daya.

“Yana da mahimmanci mu tuna yadda muke tarayya, ta hanyar imaninmu, alakar gama gari da ya kamata ta hada kawunanmu kuma kada mu yarda mu mika kanmu ga masu neman raba mu, ta hanyar amfani da manyan addinanmu guda biyu, don wani muradi nasu na kansu.

“Ya kamata mu hada kai mu yi addu’a kan munanan abubuwan da suka faru na satar mutane da fashi da makami da kuma kokarin amfani da siyasa wajen bata alakar kasar a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

“Ina kira ga shugabanninmu na siyasa da na addini da kuma sarakunan gargajiya da su karfafa wa ’yan kasar nan gwiwa don rungumar juna cikin kauna da jin kai.”

KU KARANTA KUMA: Babu rashin jituwa tsakanina da Sheikh Dahiru Bauchi - Tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi

A wani labarin, mun ji cewa shahararren malamin nan na addinin Musuluncin a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gabatar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba, 12 ga watan Mayu.

An tattaro cewa Shehin Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke garin Bauchi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa daya daga cikin 'ya'yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mabiya sallan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel