Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki

Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki

- Hukumar majalisar tarayyar Najeriya ta tsananta tsaro a majalisar sakamakon farmakin da ake zargin Boko Haram tana yunkurin kaiwa

- A saboda kalubalen tsaron, magatakardan majalisar ya fitar da takarda inda ake bayyana za a dinga caje dukkan ababen hawa

- A takardar mai kwanan watan 10 ga Mayu, an bukaci dukkan 'yan majalisar da ma'aikatanta da su bada hadin kai ga jami'an tsaro

Hukumar majalisar tarayyar kasar nan ta ja kunnen 'yan majalisa, ma'aikata, hadimansu da sauran masu ruwa da tsaki da su ankare da kalubalen tsaron da ake fuskanta, The Punch ta ruwaito.

Majalisar ta ce ta kawo matakan da zasu tabbatar da tsaro tare da gane mutum kafin a basu damar shiga farfajiyar majalisar.

An gano cewa majalisar tarayyan na daya daga cikin wuraren da 'yan ta'addan Boko Haram ke kallon kai hari.

An ga wata takarda a ranar Talata da ta gabata wacce aka mika ta ga dukkan Sanatoci, 'yan majalisar wakilai, mataimakin magatakardan majalisar, magatakarda da sauran jiga-jigan majalisar.

KU KARANTA: Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki
Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan sandan da 'yan bindigan daji suka harba ya sheka lahira a asibiti

Wannan sanarwan tana zuwa ne daga magatakardan majalisar tarayya, Amos Ojo, ta hannun sakataren cigaban ma'aikatan majalisa, Abiodun Oladoyin mai kwanan wata 7 ga Mayun 2021.

Takardar tace, "An umarceni da in sanar da dukkan 'yan majalisa da ma'aikata, ganin yadda tsaron kasar nan ke ciki da na majalisar tarayya, ya zama dole a tsananta tsaro domin gujewa shigowar miyagu cikin majalisar.

"A don haka, an umarci jami'an tsaro da su dinga duba ababen hawa da jama'ar da suke shigowa majalisar tarayyar.

“Ina bukatar 'yan majalisar da dukkan ma'aikata da su bada hadin kai ga jami'an tsaron domin su samu damar sauke nauyin dake kansu tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a majalisar tarayya."

A wani labari na daban, 'yan sanda a jihar Binuwai sun bankado wasu kaburburan sirri a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa an samo ire-ire kaburburan nan a garin ZakiBiam dake karamar hukumar Ukum tun a watan Oktoban 2019, makonni uku bayan an gano wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne ke kashe mutane tare birnesu a ciki a karamar hukumar Ushongo ta jihar.

Wannan gano kaburburan da aka yi ya biyo bayan kama wasu miyagun gagararrun 'yan ta'adda biyu da aka yi wadanda ake zargin yaran Azonto ne, mataimakin marigayi Terwase Akwaza a yankin Katsina-Ala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel