'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga 4, sun kwato shanu 170 a Katsina

'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga 4, sun kwato shanu 170 a Katsina

- 'Yan sandan jihar katsina sun damke wasu mutum hudu da ake zargi da zama 'yan bindigan da suka gallabi Kankara da kewaye

- Bayan bayanan sirrin da hukumar 'yan sandan suka samu, sun tare 'yan bindigan kuma sun kwace shanu 170 da tumaki 38

- Kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana, sunayen 'yan bindiga shine Isiya Halliru, Nasiru Bature, Bello Hamza da Hassan Iliyasu

A kalla mutum hudu aka kama wadanda ake zargi da alaka da 'yan bindigan daji, satar shanu, garkuwa da mutane tare da fashi da makami a jihar Katsina, Channels TV ta ruwaito.

Wadanda ake zargin, kamar yadda hukumar 'yan sandan jihar ta sanar, 'yan wata gagarumar kungiyar 'yan ta'adda ce da suka addabi karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina da kewaye.

A wani jawabi ga manema labarai a ranar Talata, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah yace sun kama wadanda ake zargin ne bayan bayanan sirri da suka samu a ranar 10 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis hutun Sallah

'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga 4, sun kwato shanu 170 a Katsina
'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga 4, sun kwato shanu 170 a Katsina. Hoto daga @ChannaleTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

Isah ya ce a yayin kama wadanda ake zargin, 'yan sandan sun samo shanu 170 da tumaki 38 a hannunsu.

"Dubun wasu Isiya Halliru, Nasiru Bature, Bello Hamza duk a kauyen Fanteka dake karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina ta cika tare da wani Hassan Iliyasu dake kauyen Masaurari a karamar hukumar Kankara," yace.

"Mun samu bayanan sirri cewa 'yan bindigan na tahowa ne daga wani wuri da suka tafka barna kuma cike da nasara muka yin lambo har muka kama su bayan musayar harsasai da muka yi.

"Mun kama hudu daga ciki kuma mun samo shanu 170, tumaki 38 daga wurinsu. Ana cigaba da bincikensu domin kamo sauran 'yan kungiyar."

A wani labari na daban, Dan sanda mai mukamin DSP mai suna Abdulqadir Garba Hardo, wanda wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka harba a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

Hardo wanda 'yan bindiga suka harba a kafa yayin da yake jagorantar rundunar sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a garin Tsamiya dake karamar hukumar Bagudo ta jihar.

Raunin da ya samu daga harsashin ya ratsa ta kashin kafarsa inda ya karya shi kuma ya rasu a wani asibiti dake Gusau, jihar Zamfara a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel